Ba zan yi kewar mulki ba – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana raɗe-raɗin da wasu suka tayi cewa ba ya raye, kuma wani mutum ne mai suna Jibril Aminu daga ƙasar Sudan’ ke mulkin Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, Buhari ya ce wannan batu ba abin dariya ba ne.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani shirin fim mai suna ‘Essential Muhammadu Buhari’ da aka nuna a daren Juma’a a wani liyafar cin abinci da ‘yan uwa da abokansa suka shirya domin bikin cikarsa shekaru 80 da haihuwa mai taken “Celebrating A Patriot, a Leader, an Elder Stateman”.

Shugaba Buhari wanda ya ce wasu ‘yan Najeriya sun ƙware wajen yaɗa jita jita, da abin da ba su san gaskiyarsa ba, ya bayyana cewa wannan jita-jitar, aikin wasu makiya ne.

Da wani mai hira ya tambaye shi ko ya ji jita jitar, cewa ba shi ne Buhari ba? sai ya amsa yana murmushi, “Eh! Mutane suka ce ni ɗan Sudan ne. Ban damu ba, wasu ‘yan Najeriya suna da munanan hanyoyin bayyana kansu.”

KU KUMA KARANTA:Ina marmarin komawa Daura – Shugaba Buhari

Da aka tambaye shi yadda ya samu irin waɗannan abubuwa na ban dariya, Shugaban ya ce: “A’a. ba abin dariya ba ne domin waɗanda suka yi waɗannan kalaman suna son su kasance masu baƙin ciki, suna son karkatar da hankali daga babban batun.

“Babban batunmu shi ne samar da ababen more rayuwa, sanar da mutane cewa suna buƙatar yin aiki tuƙuru don rayuwa mai kyau, suna son jin daɗin rayuwa ne kawai ba tare da samun mutuncin al’ummarsu ba da sauransu.”

Shugaba Buhari ya kuma ce ba zai yi kewar Aso rock ba, saboda ana taƙura masa, kuma ƙoƙarin da yake yi na ganin ƙasar nan ta yi kyau,amma wasu basa ganin hakan.

Da aka tambaye shi, zai yi kewar shugabanci idan ya bar mulki? Buhari ya ce: “Da kyar ko zan yi kewar da yawa. Ina tsammanin ana tursasa ni.

Na yi imani ina ƙoƙari na amma duk da haka, ba a gani. Domin akwai mutanen da suke tunanin cewa za su iya tsoratar da ni don samun abin da suke so maimakon su bi tsari mai kyau don samun duk abin da suke so su samu. Kuma wasu suna son yin wayo na maguɗi.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *