Ba zan karɓi lefe akwati 12 ba – Mahaifin wata budurwa a Kano

0
736

Wani Babban mutum a jihar Kano aka kawowa ‘yarsa lefe akwati goma sha biyu ban da ƙaramin akwati. Da aka ƙira shi ya gani, ya ce wallahi ba zai karɓa ba, sai an mayar aka kaɗa, aka raya ya ce sam sai an mayar da kayan.

Ko kun san dalilinsa na ƙin karɓa? cewa ya yi;

  1. ‘Yata ba sayar da ita zan yi ba. So nake ta yi aure a matsayin ibada ba holewa ba.
  2. Kuma ‘yata tana da ƙanne ‘yan mata, shikenan sauran ƙannenta sai su sa rai su ma sai an kawo musu akwati goma sha biyu ko sama da haka? Kuma idan Allah bai horewa mijin ba, su raina shi, su ga ya gaza?.
  3. Suturar da ya zuba a cikin lefen masu tsadar gaske, duk iyayensa da suka kawo lefen babu wacce ta saka mai tsadar su, me ya sa ya ka sa sayawa iyayensa su saka kafin ya sayawa ‘yata, idan mai arziƙi ne shi ba maƙaryaci ba.

KU KUMA KARANTA: Waliyin amarya ya sace sadaki ana tsaka da ɗaurin aure a Kano

  1. Da ace rabin kuɗin kayan lefen, abinci ya saya, shekara nawa za su yi suna cin abincin shi da matarsa kafin ya ƙare?.
  2. Yanzu da ya yi wannan lefen ya nunawa ‘yata shi mai arziƙi ne, idan zama ya yi zama tsakaninsu har ta gane abin da take zato ba haka bane, yana ganin zai yi mutunci a idonta?
  3. Shikenan yana so ‘yata ta rinƙa alfahari a cikin ƙawaye cewa babu wacce aka yiwa lefe kamar nata, wanda hakan zai jawo mata ƙiyayya da hassada a tsakanin ƙawayenta, kuma shi kansa alfaharin haramun ne.
  4. Yana daga cikin al’adar da ta haddasa zinace zinace a ƙasar Hausa, domin samari ba su da wadatar haɗa kayan lefe. Gara su keɓe da ‘yan matan nasu ya fi sauƙi.
    Na faɗa kuma babu canji ko dai a rage lefe ko kuma a dakatar da maganar aure har sai lokacin da shi da iyayensa suka fahimci abin da nake nufi.
    Idan an rage lefen an yi biki ta tare, idan yana so ya sayo mata kantin kwari ta ajiye a ɗakinta babu ruwa na, matarsa ce.

Leave a Reply