Ba za mu sayi man fetur kai tsaye daga Ɗangote ba – Dillalan Man Fetur

0
52
Ba za mu sayi man fetur kai tsaye daga Ɗangote ba – Dillalan Man Fetur

Ba za mu sayi man fetur kai tsaye daga Ɗangote ba – Dillalan Man Fetur

Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da Gas ta Nijeriya, (PENGASSAN), ta bayyana dalilin da ya sa dillalan mai suka gaza sayan mai kai tsaye daga matatar mai ta Ɗangote.

Shugaban ƙungiyar, Festas Osifo a yayin taron manema labarai a Legas a ranar Talata, ya ce batun ya ta’allaƙa ne kan farashin da NNPC ke sayan man fetur da kuma farashin da ya ke sayarwa ga dillalan man.

Osifo ya yi bayanin cewa NNPC ka iya sayan man kan Naira 950 ya kuma ya sayar da shi kan Naira 700 ga dillalan man, wanda ke sanya NNPC ke samun faɗuwa a cinikin man.

KU KUMA KARANTA:Man Fetur ɗin Ɗangote zai shiga kasuwa a makon gobe – NNPCL

Ya ce, manyan dillalai za su iya sayan man daga Ɗangote a farashin da NNPC ke saya amma za su sayar da shi ne sama da Naira 1,000.

Ya ce dillalan man sun zaɓi ssya a wurin NNPCL ne don sanun sauƙin farashi.

Osifo ya yi bayanin cewa ana bayar da wani ɗanyen man ne don biyan bashi wanda hakan yake taƙaita samar da man don amfanin cikin gida.

Leave a Reply