Ba za mu bari a wargaza ƙasa ta hanyar zanga-zanga ba – Rundunar Sojin Najeriya

0
26
Ba za mu bari a wargaza ƙasa ta hanyar zanga-zanga ba – Rundunar Sojin Najeriya

Ba za mu bari a wargaza ƙasa ta hanyar zanga-zanga ba – Rundunar Sojin Najeriya

cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Manjo-Janar Edward Buba ya ce duk da yake ‘yan Najeriya na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, to amma zanga-zangar da aka shata somawa a ranar 1 ga watan Agusta kan iya rikidewa zuwa tarzoma da tashin hankali, kamar yadda lamarin ya auku a ƙasar Kenya.

Rundunar sojin Najeriya ta yi gargaɗin cewa za ta daƙile duk wani yunƙuri na wargaza ƙasa, ta hanyar amfani da zanga-zangar da ‘yan ƙasar ke shirin farawa a wata mai fita.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Manjo-Janar Edward Buba ya fitar, ya ce duk da yake ‘yan Najeriya na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, to amma zanga-zangar da aka shata somawa a ranar 1 ga watan Agusta, kan iya rikidewa zuwa tarzoma da tashin hankali, kamar yadda lamarin ya auku a kasar Kenya.

Matasa sun bazama kan titunan birnin Nairobi suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da dokar kara harajin kayayyaki, lamarin da kuma ya rikide zuwa tashin hankali, bayan da masu zanga-zangar suka kai farmaki tare da kona wani sashe na majalisar dokokin kasar, da ma wasu kayayyakin gwamnati.

KU KUMA KARANTA:Zanga-zanga ba gudu ba ja da baya – ‘Yan Najeriya

Hakan ya sa shugaban kasar ta Kenya Williams Ruto bayyana soke sabuwar dokar tare da rusa majalisar ministocinsa, to amma hakan bai kawo karshen zanga-zangar ba. An kashe mutane sama da 50 sanadiyyar zanga-zangar ta Kenya.

“Yanayin tashin hankalin da ke faruwa ba komai ba ne illa yunkuri na wargaza kasa. A kan haka ne rundunar sojin Najeriya ba za ta zura ido tana kallo ta bari kasar ta fada a cikin irin wannan yanayi ba,” in ji Janar Buba.

Ya kara da cewa “a kan wannan kuma, jami’an soji za su tsaya kai da fata, domin tabbatar da kare kasa daga irin wannan tashin hankali.”

Wannan gargadi na rundunar sojin na zuwa ne rana daya da wani gargadin da hukumar tsaron kasar na farin kaya wato DSS ta yi, inda ta ce ta gano wata makarkashiya da ake kullawa domin ta da hargitsi a kasa.

Wasu Mabiya Ikilisiyar United Methodist Churh A Najeriya Sun Koma Global Methodist Church Saboda Kyamar Luwadi Da Madigo

An sami rarrabuwar kai tsakanin mabiya addinin kirista na ikilisiyar United Methodist Church, UMC, a Najeriya sakamakon matsayar da majalisar gudanarwar ikilisiyar ta cimma na amincewa da ayukan luwadi, madigo da auren jinsi.

Majalisar ta UMC ta yi wannan matsayar ne a babban taronta na bayan kowacce shekara hudu da ta gudanar a Amurka. To sai dai kuma da alama matsayar ba ta sami karbuwa ba a tsakanin mabiya ikilisiyar a Najeriya, wadanda suka gudanar da zanga-zangar lumana a wani taro da suka gudanar makon jiya a Bauchi da ke Arewacin Najeriya.

Wannan ya sa mabiya ikilisiyar suka kuma gudanar da wani taron a shelkwatar UMC din da ke Jalingo a jihar Taraba, inda suka yi matsayar ficewa daga ikilisiyar ta United Methodist Churh UMC, zuwa Global Methodist Church, GMC.

Bishop John wesley Yohanna shi ne Shugaban ikilisiyar da ya jagoranchi taron, ya kuma ce sun yanke shawarar sauya shekar ne saboda ba za su zauna a ikilisiyar da ta amince da luwadi, madigo da auren jinsi ba.

Bishop Yohanna ya ce “Littafin Bible ya hana, dokar kasarmu ta hana, kuma ya saba wa al’adunmu. Saboda haka mu za mu bi abin da Bible ya fada, kuma ba za mu yi abin da za mu janyo wa ‘ya’yanmu da al’ummarmu illa ba.”

To sai dai Rev Ande Emmanuel, daya daga cikin wasu kalilan da basu amince da sauya shekar ba, ya ce suna nan daram a cikin UMC, duk kuwa da cewa su ma ba su yarda da luwadi da madigo da auren jinsi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here