Ba shiga ba fita a fadar shugaban ƙasar jamhuriyar Nijar, ana zargin yunƙurin juyin mulki

1
297

Daga Ibraheem El-Tafseer

A Jamhuriyar Nijar, dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun tsare duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a riga an tantance ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi fama da juyin mulki bayan samun ‘yanci daga turawan mulkin mallaka a 1960, inda aka yi juyin mulki har sau huɗu.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ya ruwaito cewar masu tsaron fadar shugaban ƙasar sun toshe duk wata hanya ta zuwa gidan shugaban ƙasa da ke birnin Yamai, amma babu wani rahoto na zirga-zirgar sojoji ko harbin bindiga.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NEMA ta karɓi ‘yan Najeriya 146 da suka maƙale daga jamhuriyar Nijar

Haka nan lamurra na ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

A shekara ta 2021 ne aka zaɓi Bazoum a matsayin shugaban ƙasar ta Nijar.

Shugaba Bazoum na cikin shugabannin Afirka da aka yi amannar suna ɗasawa da ƙasar Faransa, wadda ta yi wa Jamhuriyar ta Nijar mulkin mallaka.

Juyin mulki na ƙarshe da aka yi a jamhuriyar Nijar ya faru ne a shekarar 2010, lokacin da aka tuntsurar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Tandja Mamadou.

Haka nan ƙasar na fama da matsalar masu iƙirarin jihadi waɗanda ke tayar da ƙayar baya, lamarin ya yi ƙamari a wasu ƙasashen yammacin Afirka da dama, kamar Mali.

1 COMMENT

Leave a Reply