Ba mu muka ƙara farashin man fetur ba — Gwamnatin Tarayya

0
56
Ba mu muka ƙara farashin man fetur ba — Gwamnatin Tarayya

Ba mu muka ƙara farashin man fetur ba — Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ba ita ta ƙara farashin litar man fetur ba.

A ranar Laraba ne kamfanin mai na ƙasa, NNPCL ya sanar da ƙarin litar man fetur daga Naira 897 zuwa sama da Naira 1,030 a faɗin ƙasar, lamarin da ya haifar da cece-kuce da kuma alla-wadai ga ‘yan ƙasar.

Sai dai kuma a hirar da ya yi da Daily Trust, Ministan Yaɗa Labarai da Tarbiyyar Al’umma, Mohammed Idris ya ce ba gwamnati ba ce ta ƙara farashin mai.

KU KUMA KARANTA:NLC ta caccaki gwamnatin tarayya kan ƙara farashin man fetur

A cewar Ministan, NNPCL ne ya ƙara farashin man duba da yanayin da ɓangaren mai ya samu kansa a ƙasar.

Mohammed ya ƙara da cewa ba gwamnati ba ce ta baiwa NNPCL umarnin ƙarin farashin man ba saboda “gwamnati ba ta da ikon kari ko ragin farashin mai bisa ga yarjejeniyar da ke kunshe a sabon kundin dokar mai,”

Ya ce tun da aka cire tallafin mai a watan Mayun 2023, NNPCL ke cika gibin da ake samu don a saukaka farashin, “inda yanzu kuma NNPCL ya ce bashi da halin ci gaba da cike gibin.”

Leave a Reply