Daga Ibraheem El-Tafseer
Mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya faɗa wa manema labarai cewa a yanzu haka gwamnan yana hutu saboda haka bai da masaniya a kan sakin ko shari’ar ‘yar Tiktok Murja.
Idan ba a manta ba, a safiyar ranar Lahadi ne, ake ta raɗe-raɗin cewa fitacciyar ‘yar Tiktok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya ta yi ɓatan dabo daga gidan gyaran hali a Kano. Jama’a sun cika da mamaki ganin cewa ta yaya za’a ce an neme ta an rasa. Sai dai idan an sake ta ne da gangan.
Maganganu da dama suna ta fitowa daga bakin jama’a. Sai dai Kakakin gidan gyaran halin, ya shaida wa manema labarai cewa “tun ranar Alhamis mu ka saki Murja bisa umarnin kotu’
Kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano AC Misbahu Kofar Nassarawa ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewa sananniyar ‘yar Tiktok Murja Kunya ba guduwa ta yi daga gidan gyaran hali ba.
A cewar sa, tun ranar Alhamis takarda ta zo daga kotu don neman a sake ta, kuma gidan yarin ya sake ta a ranar.
KU KUMA KARANTA: An saki Murja Kunya daga gidan gyaran hali
Ya ƙara da cewa kotu ce ta kawo ta ajiya a wajensu, kuma kotu ce ta ce su sake ta.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta ce ba ta da hannu a sakin fitacciyar ‘yar Tiktok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya.
Yanzu haka dai al’umma sun shiga ruɗanin da hannun waye Murjan ta fita.