Ba ma goyon bayan amfani da ƙarfi kan Nijar, malaman Najeriya suka faɗa wa Tinubu

0
521

Daga Ibraheem El-Tafseer

Majalisar malaman addinin Musulunci a Najeriya ta gana da Shugaba Bola Tinubu a yammacin Laraba, inda suka shaida masa rashin goyon bayansu wajen amfani da ƙarfin soja kan rikcin siyasar Jamhuriyar Nijar.

Sakataren ƙungiyar Jama’atu Nasrul Islam (JNI), Farfesa Khalid Abubakar, ya bayyana cewa sun nemi shugaban ya ci gaba da lalubo hanyoyin sasanta lamarin ta hanyar difilomasiyya maimakon ƙarfin soja.

“Mun faɗa masa cewa ɗaukar matakin soja ba zai warware komai ba, kuma mun faɗa cewa ba mu goyon baya,” kamar yadda ya faɗa wa manema labarai bayan ganawar tasu.

KU KUMA KARANTA: Ba mu kai wa jamhuriyar Nijar hari ba – Faransa

“Najeriya da Nijar kamar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. ‘Yan uwa muke, addininmu ɗaya, al’adunmu ɗaya. Dole a bi a hankali don a samu zaman lafiya” inji su.

Leave a Reply