Ba a tsara ƙudirin sauye-sauyen haraji domin tauye arewa ba – Fadar Shugaban Najeriya

0
37
Ba a tsara ƙudirin sauye-sauyen haraji domin tauye arewa ba - Fadar Shugaban Najeriya

Ba a tsara ƙudirin sauye-sauyen haraji domin tauye arewa ba – Fadar Shugaban Najeriya

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 sun yi fatali da ƙudirin, musamman don gyaran da ake shirin yi a kan sauya tsarin rabon harajin sayen kayayyaki (vat) zuwa wanda zai rika la’akari da asalin inda kayan ya fito.

A yau Alhamis fadar shugaban kasar najeriya ta ca ba’a tsara kudirin dake gaban majalisun tarayyar najeriya akan sauye-sauyen haraji domin tauye jihohin arewacin kasar 19 ba.

A sanarwar da ya fitar a yau Alhamis, kakakin Shugaban Najeriya, Bayo Onanuga, yace an tsara sabon tsarin, kamar yadda aka bayyana a cikin kudirin, yayi adalci ga dukkanin jihohin da zasu amfana da shi.

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya naɗa muƙaddashin babban Hafsan Sojin Najeriya

Onanuga ya kara da cewa sauye-sauyen da ake yi na nufin gyara rashin daidaiton dake tattare da tsarin da ake amfani da shi na la’akari da asali wajen rabon harajin VAT din da aka tattara.

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 sun yi fatali da kudirin, musamman gyaran da ake shirin yi a kan sauya tsarin rabon harajin sayen kayayyaki (VAT) zuwa wanda zai rika la’akari da asalin inda kayan ya fito.

A cewar Onanuga, an kirkiri sabuwar manufar ne da nufin yiwa harkar gudanar da tsarin harajin Najeriya garanbawul, da inganta shi tare da kawar da duk wata gaba da ba ta da amfani a tsarin harajin kasar.

Ya kara da cewa bijiro da sauye-sauyen na da matukar mahimmanci ga rayuwar ‘yan Najeriya kuma Shugaba Tinubu bai kirkiresu domin tauye wani bangare na kasar ba.

Leave a Reply