Ba a kashe Ba’amurke a Anambara ba – ‘Yan sanda

0
190

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambara ta musanta rahotannin kashe wasu ‘yan ƙasar Amurka a jihar.

Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar talata a Onitsha, ya ce babu wani Ba’amurke da ke cikin ayarin motocin da ‘yan bindiga suka kai wa hari a ranar talata.

‘Yan bindigar sun buɗe wuta kan ayarin ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka da ke ƙaramar hukumar Ogbaru a jihar.

Mista Ikenga, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce an kashe ‘yan sandan tafi da gidanka biyu da ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka da ke cikin ayarin motocin tare da ƙona gawarwakinsu da motocinsu.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Najeriya da ya auri Ba’amurkiya, ya shiga aikin soja a Amurka

A cewarsa, rundunar haɗin guiwa ta jami’an tsaro ta fara aikin ceto tare da ƙwato ‘yan bindigar domin zaƙulo ‘yan bindigar. “Bayan harin da aka kai wa ayarin ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka da misalin ƙarfe 3:30 na rana a kan titin Atani, Osamale.

“Yan bindigar sun kashe jami’an PMF biyu, da ma’aikatan ofishin jakadancin biyu, tare da ƙona gawarwakinsu da motocinsu.

“Har ila yau, masu ƙone-ƙone da masu kisan gilla da suka ga jami’an tsaro na haɗin guiwa sun yi awon gaba da jami’an ‘yan sanda biyu, direban mota ta biyu kuma suka tafi da su.

“Babu wani Ba’amurke da ke cikin ayarin motocin,” in ji shi. Mista Ikenga ya ce rundunar ta damu da cewa irin waɗannan jami’ai za su ziyarci jihar ba tare da tuntuɓar ‘yan sanda a yankin ko wata hukumar tsaro ba.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a ci gaba da yaƙi da masu tada ƙayar baya a jihar har sai an samu kwanciyar hankali.

Leave a Reply