APC ta ceto Najeriya daga wargajewa, Tunibu zai ɗora ya magance matsalar tsaro – Shinkafi

1
448

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi, ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba Najeriya za ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda ta kasance kafin bullar kungiyoyin boko haram da ‘yan fashi da kuma kungiyar IPOB.

Shinkafi, wanda ya bayar da wannan tabbacin a ranar Lahadi, a lokacin da yake ƙaddamar da yakin neman zaben Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, ya ce gwamnatin APC mai ci ta ceto ƙasar nan daga wargajewa.

Ya kara da cewa, Nijeriya a matsayin ta na kasa me ‘yan ci na shirin rugujewa saboda saurin karuwar manyan masu aikata laifuka ke yi, musamman a arewa maso gabashin ƙasar inda aka kashe dubban rayukan da ba su ji ba ba su gani ba.

KU KUMA KARANTA:Cikin Hotuna: Yadda aka yi jana’izar ɗan majalissar da ya rasu a taron Tinubu a Jos

“Abin da ’yan kasar mu suka kasa fahimtar dalilin da ya sa matsalolin rayuwa a ƙarkashin wannan gwamnati shi ne, abin da ya fi muhimmanci shi ne a yi la’akari da yaƙi, da ƙalubalen tsaro da ke addabar kasar wanda aka fara tun gwamnatin da ta gabata.

“Babu wani ci gaba mai ma’ana da za a samu ba tare da zaman lafiya ba, don haka dole ne gwamnatin Buhari ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin Najeriya ta dore, kafin ta gudanar da ayyukan da ke kunshe cikin tsarin,” in ji Shinkafi.

Shinkafi ya ci gaba da cewa, yaki da masu aikata laifuffuka wanda ba a san su waye ba, yana da dabaru daban-daban, lamarin da ake kyautata zaton ya dauki wannan gwamnati kusan shekaru takwas, har zuwa kwanan nan da jami’an tsaro suka samu nasarar yaki a yankin arewa maso gabas, yayin da a halin yanzu suke yaƙin a yankin arewa maso yamma na yaƙi da ‘yan fashi.

“Zuwar Ahmed Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa na gaba, idan aka zaɓe shi, zai karɓa daga wannan gwamnati, domin zai karfafa nasarar da aka samu a kan masu aikata laifuka, kuma duk abubuwan da ake sa ran ‘yan ƙasa su samu, za su biyo baya”, Shinkafi ya tabbatar.

Da yake jawabi, Sanata Sahabi Ya’u, ya yi kira ga dukkan waɗanda suka cancanci kada kuri’a a fadin mazabarsa ta Sanata, da suka hada da kananan hukumomin Kaura Namoda, Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji, da su yi amfani da kuri’unsu domin ci gaba da samun ci gaba a shiyyar.

1 COMMENT

Leave a Reply