APC na daf da karɓar jiga-jigan NNPP ciki har da ‘yan majalisa – Ganduje

0
14
APC na daf da karɓar jiga-jigan NNPP ciki har da 'yan majalisa - Ganduje

APC na daf da karɓar jiga-jigan NNPP ciki har da ‘yan majalisa – Ganduje

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tarbar masu sauya sheƙa daga wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP, wacce ya bayyana a matsayin “jam’iyyar da ke dab da mutuwa.”

Ganduje ya bayyana hakan jiya yayin rabon motocci 63 da babura 1,137 ga shugabannin APC na kananan hukumomi da mazabu a faɗin Jihar Kano. Wannan shiri na ƙarfafa jam’iyya da tallafa wa mambobinta ya samu ɗaukar nauyi daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin.

“Wannan shirin tallafa wa al’umma ba wai ga mambobin APC kaɗai ba ne, har ma da al’ummar Kano baki ɗaya. Zai taimaka wajen inganta rayuwar mutane da samar da ayyukan yi,” in ji Ganduje.

KU KUMA KARANTA:Za mu yiwa filin jirgin saman Legas ginin zamani – Ganduje

Ganduje ya jinjinawa mambobin jam’iyyar saboda ƙwazon su da biyayya, yana mai nuna tabbacin cewa wasu manyan jiga-jigai, ’yan majalisa da sanata-senata daga NNPP za su sauya sheƙa zuwa APC nan ba da jimawa ba.

“Dubban mutane na shirin shigowa cikin wannan babbar jam’iyya. Nan bada daɗewa ba za mu tarbi wasu fitattun jiga-jigai daga waccan jam’iyya da ke dab da mutuwa” Ganduje ya bayyana.

Ya kuma yaba da jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun rage farashin mai, farashin abinci, tare da ƙarfafa darajar Naira.

Leave a Reply