Daga Ibraheem El-Tafseer
(eltafseerpen@gmail.com)
Kafar sadarwa ta Facebook, ɗaya ne daga cikin kafofin sadarwa na zamani wanda ake yaɗa saƙonni a soshiyal midiya cikin gaggawa. Facebook, ɗaya ne daga cikin ‘applications’ (manhajoji) dangogin su Twitter, Instagram, Telegram, Snapchat da sauransu. Kamar a Nijeriya kam, Facebook ya fi shahara a yanzu, tun da an rufe kafar sadarwa ta Twitter. Ana yiwa Facebook laƙabi da kafar sada zumunta.
Tun da a Facebook ana iya haɗuwa da mutanen da ba a sansu ba, kuma a ƙulla alaƙa mai ƙarfi, har ta kai an ziyarci juna, daga nisan garuruwa. Facebook yana haɗa zumunci sosai, sannan yana raba zumunci sosan gaske.
Nasan ba sabon abu bane, haɗuwa ta dalilin Facebook har a ziyarci juna daga nisan jihohi a faɗin Nijeriya. Wannan ya sha faruwa, akwai dalilai da yawa kan haka.
KU KUMA KARANTA: Yadda ake tantance (Verifying) Facebook account da Facebook Page
Kuma zumunci ya ƙullu yadda har idan wani abin farin ciki ko na baƙin ciki ya faru da ɗaya, sukan ziyarci juna. Facebook yana haɗa zumunci tsakanin namiji da mace har ya kai ga sun yi aure. Ni ma akwai abokina da dalilin Facebook suka haɗu da matar da ya aura, kuma har yanzu suna tare. Facebook yana haɗa abubuwa da yawa har da baɗala.
Akwai group-group ɗin na sada zumunta da yawa a Facebook, wanda ya haɗa mutane da dama, maza da mata, ana kuma sadar da zumunta ɗin.
Misalin ɗaya daga cikin irin waɗannan group ɗin shi ne group ɗin ‘Home Of Solace’ wanda ko a shekaru biyu baya sun shirya taro, kuma da yawa daga cikin ‘yan group ɗin sun halarta, an ci, an sha, an yi raha, sannan aka ɗauki hotuna. Zumunci ya ƙullu tsakanin da dama daga cikinsu.
Facebook wani wuri ne da mutane suke rubuta ra’ayoyinsu da nufin isar da saƙo, cikin harsunan da suke buƙata saƙon ya isa. Kamar mu a nan Nijeriya, an fi yin rubutun da yarukan Hausa, Turanci, Larabci da Faransanci. Da farko idan mutum ya buɗe shafin Facebook, akwai buƙatar yasan da wane dalili ya buɗe shafin Facebook ɗin.
Idan saƙo yake so yana isarwa, to sai ya duba ya ga da wane yare ya kamata ya yi rubutu wajen isar da saƙon, domin saƙon ya isa ga wanda aka yi dominsu. Wasu suna hawa Facebook ne don su karanta labarai da sauransu. Wasu kuma suna hawa Facebook ne don su ci mutuncin wasu.
Akwai Gidauniyoyi (Foundations) na neman taimako da yawa da suke sako hotunan waɗanda ake nema wa taimakon a shafukansu na Facebook. Kuma tabbas ana samun taimakon sosai a Facebook ɗin. Akwai misalai da yawa kan haka. Hajiya Fauziyya D. Sulaiman ɗaya ce daga cikinsu.
Facebook ya kasance wajen samun labarai cikin gaggawa. Kusan dukkan kafafen yaɗa labarai na jaridu da gidajen Talabijin da Rediyo duk suna da shafi a Facebook wanda suke wallafa labaransu a ciki. Da zarar labari da ɗumi-ɗumi ya samu, za ka ga suna ta rige-rige wajen wallafa wa a shafukansu.
Hakan yasa mafi yawan labarai a Facebook ake fara gani, kafin a samu cikakken labarin daga baya. Facebook ɗin kuma ya shahara wajen kawo labarai na ƙanzon kurege, shi ya sa da yawan mutane ba sa yarda da labaran Facebook, har sai sun ga wata jarida ta gaske ta wallafa labarin a shafinta.
Abin da ya sa nace jarida ta gaske shi ne, jaridun bogi suna nan birjik a Facebook. Da zarar mutum ya sayi babbar waya, to shi ma ya zama ɗan jarida. Abin da yake ta faruwa kenan yanzu a Facebook da WhatsApp.
Wasu kuwa suna hawa Facebook ne don ganin labaran ban dariya (comedy), don nishaɗi da rage damuwa. Wasu kuma fasadi kawai suke yaɗa wa a Facebook. Ko kunya babu za ka ga suna ta furta kalaman batsa da rashin tarbiyya iri-iri a bidiyo su ɗora a Facebook da sunan tallan magani ko kuma yaɗa iskanci.
Haka kuma Facebook ya zama wajen hada-hadar kasuwanci iri-iri. Kusan dukkan masu manyan masana’antu, da masu manyan shaguna har da masu matsakaitan kasuwanci, duk suna da shafuka da suke tallata harkokin kasuwancinsu ta hanyoyin rubuce-rubuce a Facebook, haɗe da hotuna da Bidiyon yadda kasuwancin nasu yake.
Za mu ci gaba…
[…] KU KUMA KARANTA: Anya Facebook dandalin sada zumunta ne kuwa? (I) […]