Annobar tsutsa ta mamaye gonakin Tumatir a Najeriya

0
27
Annobar tsutsa ta mamaye gonakin Tumatir a Najeriya

Annobar tsutsa ta mamaye gonakin Tumatir a Najeriya

Daga Shafa’atu Dauda Kano

Ƙungiyar Manoman Tumatir ta Najeriya ta bayyana fargaba mai tsanani game da ƙarancin tumatir a kasuwanni da kuma yiwuwar tsadar sa a bana, sakamakon annobar wata mummunar tsutsa da ta mamaye gonaki a sassa daban-daban na ƙasar.

Wannan annoba, wacce ta samo asali daga bullar wani nau’in tsutsa mai haɗari da ake kira Tuta absoluta, ta yi mummunar barna a gonakin tumatir, musamman a jihohin Kano, Jigawa da Bauchi, inda dubban manoma suka yi asarar miliyoyin naira da suka zuba a noman.

Shugaban Ƙungiyar Manoman Tumatir ta Jihar Kano kuma Sakataren Ƙasa na Ƙungiyar, Alhaji Sani Danladi Yada-Kwari, ya bayyana Cewa

“Musamman a nan Kano, barnar da tsutsar ta yi matuƙa girma. Duk manomin da ya dasa tun watan Nuwamba ko Disamba bai samu komai ba. Akwai wanda timatir dinsa ya kusa girma, amma cikin kwana uku kawai tsutsar ta shanye shi baki ɗaya.”

Alhaji Yada-Kwari ya ƙara da cewa a halin yanzu ana ci gaba da tattara alkaluman asarar, amma hasashe ya nuna cewa manoman jihar Kano kaɗai sun yi asarar da ba ta gaza naira biliyan 20 ba.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin tarayya haɗe da ISDB, AFDB za su tallafawa manoma ƙarƙashin shirin SAPZ a Kano

Baya ga barazanar da tsutsar ta kawo ga manoma, sakataren Ƙungiyar Masu Hada-hadar Tumatir a kasuwar ‘Yan Kaba, Malam Alin Bello, ya bayyana cewa yanzu haka akwai karancin tumatir a kasuwanni, kuma da kyar ake samun wanda bai lalace ba.

Basoda baya da kyau. Mutane da yawa ba sa iya saye saboda yawan lalacewa. Idan aka kawo shi kasuwa ba a sayar ba, kafin yamma tsutsar ta gama cinye shi,” in ji shi.

Masana sun bayyana cewa yanayin zafi na taimaka wa yaduwar tsutsar, wadda ke da ƙyar magani, domin tana saurin garkuwa daga sinadaran kashe kwari da ake amfani da su.

Ƙungiyar Manoman Tumatir ta ƙara yin kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo agaji da matakan dakile yaduwar wannan tsutsa, tare da ba manoma horo da kayan aiki domin kare gonakinsu daga annobar nan gaba.

Ina roƙon gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su taimaka. Manoma sun shiga mawuyacin hali,” a cewar Alhaji Yada-Kwari.

Tsutsar Tuta absoluta na ci gaba da zama babban barazana ga samar da abinci da kuma tattalin arzikin manoma a Najeriya.

Leave a Reply