Ana ƙarancin kwaroron roba a Kenya

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kenya na fama da ƙarancin kwaroron roba (Condom) da take rabawa kyauta ga maza saboda rashin tallafi da take fuskanta daga ƙungiyoyi. Ƙasar na buƙatar aƙalla kwaroron roba miliyan 400 a kowacce shekara.

Gwamnati a yanzu na iya raba kwaroron roba miliyan 150 ne kacal, wanda bai kai rabin abin da ake buƙata ba.

Gidauniyar AIDS Foundation, ta yi gargaɗin cewa idan ba a shawo kan matsalar ba, Kenya na iya fuskantar kalubalen yaɗuwar cututtuka irinsu HIV, da cutar da ke yaɗuwa ta jima’i da ɗaukar cikin da ba a so.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC da Ma’aikatar lafiya a jihar Yobe sun yi taro kan cutar tamowa

Wani babban jami’i a hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ya ce akwai buƙatar ɗaukan matakai a cikin gaggawa.

Ƙwararru a fannin lafiya da ‘yan majalisa da ƙungiyoyin tallafi za su gudanar da wani taro nan da kwanaki uku a birnin Mombasa domin shawo kan matsalar da kuma samar da ƙarin magungunan HIV.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *