Ana zargin tsoffin shugabannin Najeriya Obasanjo da Buhari da awun gaba da dala biliyan 6 na kwangilar wutar Mambilla

0
5

Daga Ibraheem El-Tafseer

Tsofaffin shugabannin Najeriya Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari na ba da shaida a gaban ƙungiyar ‘yan kasuwa ta ƙasa da ƙasa (ICC) da ke birnin Paris na ƙasar Faransa kan zargin awun gaba da dala biliyan 6 na kwangilar wutar lantarki ta Mambilla.

Dangane da tuhumar da ake yi na yin sulhu da gwamnatin tarayya na dala biliyan 2.3 da Sunrise Power ta shigar a kan Najeriya kan zargin karya kwangilar da gwamnatin tarayya ta yi.

Majiyoyi sun tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa shugabannin biyu suna birnin Paris dangane da lamarin.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure mutane 4 da ake zargi da satar birkin jirgin sama guda 80

Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya karyata daren Asabar da ta gabata cewa, fadar shugaban kasar ta tilastawa wasu fitattun ‘yan Najeriya bayar da shaida a shari’ar da ake yi a birnin Paris.

Leave a Reply