Ana tuhumar wani Malami da auren mata 75

2
216

Jami’an Tsaro a jamhuriyar Nijar sun damƙe wani Malamin addinin musulunci mai suna Malam Gausi Almustapha bisa zargin sa da wuce gona da iri, inda ya auri mata saba’in da biyar kamar yadda aka ruwaito.

Malamin wanda yake zaune a ƙauyen Tudun Faira a yankin Dogon-Dutse na Jihar Dosso, ya yi ƙaurin suna, inda yake iƙirarin cewa shi ne Mahadi, wanda zai zo a ƙarshen duniya.

KU KUMA KARANTA: Allah ɗaya gari bam bam! Gizo-Gizo, abincin yau da kullum a Kambodiya

Haka kuma hukumomin na tsaro sun zarge shi da laifin bautar da mabiyansa, inda yake sanya su aikin noma a manyan gonakinsa. Yana kuma aure ‘ya’yansu ba tare da bin tsarin Shari’ar Musulunci ba.

A halin da ake ciki dai, malamin yana tsare a gidan maza, inda ake shirin yanke masa hukunci.

2 COMMENTS

Leave a Reply