Ana ta sukar ‘yan majalisun Najeriya kan ware wa kansu maƙudan kuɗaɗe

0
387

Daga Ibraheem El-Tafseer

‘Yan Najeriya sun fara sukar ‘yan majalisar dokokin ƙasar kan matakin da suka ɗauka na ware wa kansu Naira biliyan 70 daga cikin biliyan 500 ɗin da suka amince a kashe wajen bai wa ‘yan ƙasar tallafin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta yi.

Ita dai Majalisar ta ce ta yi hakan ne, domin inganta yanayin aiki na sabbin membobinta, waɗanda wannan ne zuwansu na farko majalisar, don haka suna buƙatar su samu don abin tasarufi kafin komi ya daidaita.

Matakin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce da kuma martani inda ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’Adam ta SERAP ta yi barazanar kai ƙara kotu matuƙar ba a janye kuɗin da ‘yan majalisar suka amince wa kansu ba.

KU KUMA KARANTA: Ba a ƙara wa shugaban ƙasa, mataimakinsa, zaɓaɓɓun ‘yan majalisa da alƙalai albashi ba – Gwamnatin tarayya

Ita ma ƙungiyar CAJA, mai fafutukar tabbatar da adalci da daidaito a Najeriyar ta yi shuri da matakin, da ta bayyana a matsayin rashin tausayi ga halin da ‘yan ƙasar suka samu kansu a ciki.

”Wannan abun mamaki ne, kuma ya yi wuri, a ce sun fara fito da zalamarsu a fili, tun da an zaɓo su ne domin su tsara dokoki da za su fitar da ‘yan Najeriya daga halin ƙuncin da suke ciki, yanzu wasu na ganin ƙoƙari suke yi su mayar da kuɗin da suka kashe a lokacin yaƙin neman zaɓe” in ji shi.

Da yake kaso 70 cikin 100 na ‘yan majalisar sabbi ne, wasu daga cikinsu na ƙorafin cewa har sun fara cin bashi, saboda rashin abin da za su yi amfani da shi wajen riƙe kansu, da kuma tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

Sai dai a cewar Kwamared Dakata, yawancinsu dama sun fi ƙarfin abin da za su rayu da shi na yau da kullum, kuma akwai buƙatar su sadaukar da kansu wajen hidimta wa jama’a, ba wai wata dama ce suka samu ta holewa ba.

Wasu bayanai dai na cewa wannan adadi na Naira biliyan 70 da ‘yan majalisar suka ware wa kansu, ya zarce wanda aka ware wa manoma cikin tallafin rage raɗaɗin.

Shi ma Kwamared Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC mai sanya ido kan harkokin majalisun Najeriyar, ya ce abin da ‘yan majalisar suka yi garaje ne.

”A halin da ake ciki su kansu ‘yan Najeriya da dama ba sa samun abinci, ba sa iya biyan kuɗin makaranta, amma su yanzu daga zuwansu tun ma ba su fara aikin komai ba sun fara nema wa kansu mafita.”

Ya ce idan ma za su yi haka, da sai su jira su fara aiki a fara ganin amfaninsu ga jama’a tukuna.

Ita dai gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ta ce za ta shafe watanni shida ne tana raba wa mutane miliyan 12 Naira dubu takwas duk wata, domin ganin arziƙi ya yaɗu.

Leave a Reply