An ɗaure wani Malami a Saudiyya shekara 20 kan sukar gwamnati
Saudiyya ta yanke wa wani malami Asaad Al-Ghamdi mai shekara 47 hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari saboda sukar gwamnati a shafukan sada zumunta.
An kama shi a watan Nuwamban 2022 a birnin Jeddah, kuma aka yanke masa hukunci a ranar 29 ga Mayu a wata kotu ta musamman, inda aka zarge shi da ta’addanci.
Takardun kotu sun nuna cewa an tuhumi Ghamdi da “ƙalubalantar addini da adalcin Sarki da Yarima” da “wallafa jita-jita da labarun ƙarya.”
Shaidun da aka gabatar sun haɗa da rubuce-rubucen da ya suka soki ayyukan ‘Vision 2030’ da nuna alhininsa ga mutuwar ɗan gwagwarmaya Abdallah al-Hamed.
KU KUMA KARANTA: Saudiyya na son fara shigar da naman shanu da waken suya ƙasarta daga Najeriya
Lamarin Ghamdi ya yi kama da na ɗan uwansa Mohammad, wanda aka yanke wa hukuncin kisa a bara saboda yaɗa wasu rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta.
Ɗan uwansu na uku, Saeed, wanda malamin addini ne da ke gudun hijira, ya yi Allah-wadai da hukuncin, inda ya ce babu komai game da tuhume-tuhumen face zalunci.
A cikin ’yan shekarun nan, kotunan Saudiyya sun yanke hukuncin ɗaurin shekaru masu tsawo ga mutane da dama saboda rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta, ciki har da Nourah al-Qahtani da aka yanke wa hukuncin shekara 45 da Salma al-Shehab da aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara 34.
Akwai Manahel al-Otaibi, wadda aka yanke wa hukuncin shekara 11 saboda ƙalubalantar dokokin Saudiyya game da sanya sanya abaya ga mata.