An yi wa Fasto ɗaurin rai da rai bayan yayi wa yaya da ƙanwa ciki

0
491

Daga Abbas Ɗalibi, Legas.

A ranar talata ne wata kotun laifuka da ke Ikeja a Legas ta yanke wa wani Fasto mai suna Nduka Anyanwu mai shekaru 51 hukuncin ɗaurin rai da rai bayan a same shi da laifin yin lalata da wasu mata biyu ‘yan uwan har ya kai ga ya yi masu ciki.

Mai shari’a Abiola Soladoye ya yanke hukuncin ne bayan samun Anyanwu da aikata laifin.

Gwamnatin Legas ce ta gurfanar da Faston a ranar 17 ga Afrilun2022, a kan tuhume-tuhume biyu, bayan ya aikata laifin a tsakanin shekarar 2019 zuwa Agustan 2020 a titin Aowojobe, a yankin Oshodi na jihar.

A cewar mai gabatar da qara, laifin yana da hukunci a karkashin sashe na 137 na dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.

Wanda ake tuhumar ya ƙi amsa laifinsa lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotu, kuma mai gabatar da ƙara ya gabatar da shaidu shida, yayin da wanda ake tuhuma wa kansa ya kuma bada shaida shi kadai.

A lokacin shari’ar, mai gabatar da ƙara na farko ta shaida cewa, duk da cewa tana da shekaru 15 a duniya, tana da shekaru 13 a lokacin da lamarin ya faru, ta shaida cewa wanda ake zargin ya san ta a matsayin limamin cocinsu, kuma yana lalata da ita, ya kuma gargaɗe ta da kada ta gaya wa kowa, kuma ya ce ba za ta yi ciki ba, amma daga ƙarshe ta samu juna biyu ta kuma haife masa ɗa na miji.

‘Yar uwar wacce ta gabatar da shaida ta farko, wacce a yanzu take da shekaru 19, amma tana ’yar shekara 17, lla lokacin da lamarin ya faru, ta bada shaida ta biyu, ta haɗa kai da wacce ta bada shaida ta farko cewa wanda ake tuhuma fa Fasto ne da yayi ta lalata dasu.

Ta kuma ba da labarin yadda wanda ake tuhumar ya yi lalata da ita da izinin iyayenta, cewa zai kai ta da ‘yar uwarta qasar waje.

KU KUMA KARANTA:Yadda yaro ɗan shekara 17 ya yiwa mata 10 ciki

Mahaifin waxanda abin ya shafa, a cikin shaidarsa, ya bayyana cewa ya san wanda ake ƙara, kasancewar shi ɗan coci ne,kuma abokinsa ne, cewa shi ke da alhakin yin cikin ga ‘ya’yansa mata biyu.

Ya ce yana sane da cewa wanda ake tuhumar yana lalata da ‘ya’yansa mata.

Mahaifiyar wadanda lamarin ya rutsa da su, a shaidarta, ta bayyana cewa, ta kaɗu matuka bayan da ta gano cewa mutum ɗaya ne ya yi wa ‘ya’yanta mata biyu ciki.

Anyanwu, wanda ya bayar da shaidar a kariyar sa, ya ce mahaifin yaran ne ya ba shi su a matsayin matansa, kuma yana saduwa dasu.

A yayin da yake yanke hukunci, alqalin ta ce masu gabatar da ƙara sun iya sauke nauyin hujjojin da aka ɗora musu, kan laifin kazanta.

Mai shari’a Sholadoye ta ce abubuwa uku na kazanta, sun haɗa da cewa yaran, shekarunsu bai kai ba, wanda ake tuhuma ya yi jima’i da su kuma tamkar azabtarwa ne a garesu.

Ta ce, “Na gamsu da shaidar da aka nuna cewa wanda ake tuhuma yana da laifi kamar yadda ake tuhumarsa da laifin lalata.

“‘Yan sandan sun yi watsi da alhakin da ya rataya a wuyansu ta hanyar kin tuhumar mahaifin yaran, tare da wanda ake tuhuma” inji ta.

Ta ce Iyayen yaran suna da alhaki wajen rikon sakainar kashi wajen tarbiyyar yaran, sakacin yaran nasu ya sa yanzu sun zama kakanni kuma ɗawainiya ta ƙaru akansu.

” Kamata ya yi a sanyawa iyayen takunkumi a gurfanar da su gaban kuliya.

“Iyayen yaran biyu, sun yi rashin gaskiya ta yadda suka bar wani abokinsu fasto ya yaudare su cewa zai taimaka musu su kai ‘ya’yansu kasashen waje alhali wanda ake qara ba zai iya taimakon kansa ba”.

Ta ƙarar Nduka Anyawu, a nan ne aka yanke maka hukuncin daurin rai da rai, dangane da kirga na ɗaya da na biyu, hukuncin zai ci gaba da tafiya tare, ta kuma bada umarnin rubuta sunansa a cikin rajistar masu laifi na jihar Legas.

Leave a Reply