Hamas ta nuna mana ba mu da wayo wajen miƙa gawarwakin mutanen mu da ta yi garkuwa da su – Isra’ila
Isra’il ta tabbatar da cewa gawar mutumin da Hamas ta miƙa mata a ranar Litinin ba ta cikin gawarwakin da ƙungiyar ta yi garkuwa da su da aka tsara za ta mayar da su.
Har yanzu dai ana neman gawarwaki 13 daga cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su, waɗanda ake tunanin za ta miƙa domin cika sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da Shugaba Trump ya tsara domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Isra’ila ta ce wannan gawar da aka miƙa mata na cikin waɗanda ake tunanin an yi garkuwa da su, suka mutu a Gaza aka binne su a can.
KU KUMA KARANTA: Ana ci gaba da musayar fursinoni tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas
Hukumomin Isra’ila na dai ganin wannan a matsayin yunƙurin Hamas na karya alƙawarin da aka shiga domin kawo ƙarshen yaƙin.
Yanzu haka dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yana ganawa da jami’an gwamnatinsa domin tattauna matakin da zai ɗauka.
Daga cikin matakan da ake tunanin Isra’ila za ta ɗauka akwai ƙara faɗaɗa wuraren da take da iko da su a Gaza.









