An yi bikin binne Sam Nujoma a Namibia

0
33
An yi bikin binne Sam Nujoma a Namibia

An yi bikin binne Sam Nujoma a Namibia

Daga Idris Umar Zariya

Shi bikin binne shin ya samu halartar mai ɗakinsa da ’ya’yansa da jikokinsa, haɗi da wasu shugabannin Afirka na da da na yanzu, wanda aka gudanar a makabartar Heroes Acre.
Bincike ya nuna cewa manyan masu riƙe da madafun ikon ƙasar dai, sun bayyana Nujoma a matsayin mai kishin Afirka, kuma mutum ne mai kishin ƙasa wanda ya kare nahiyar Afirka daga tsarin mulkin mallaka.

Mutane da dama ne daga sassan ƙasar suka taru tun da sanyin safiya a Heroes Acre da ke babban birnin Windhoek, domin nuna alhinin tafiyar Nujoma wanda ya rasu makonni biyu da suka gabata yana da shekaru 95 a duniya.

KU KUMA KARANTA:Tsohon shugaban Namibia Sam Nujoma ya rasu

Mamacin Ana kallonsa a matsayin na karshe daga cikin shugabannin da suka rage na waɗanda suka jagoranci gwagwarmayar kawo ƙarshen masu mulkin mallaka da kuma fafutukar neman ‘yanci a fadin nahiyar.

Nujoma wanda ya yi wa’adi uku a matsayin shugaban ƙasa daga shekarar 1990 zuwa 2005, ya yi suna wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Namibia.

Namibia ta yi zaman makoki na kwanaki 21, inda aka sauke tutocin ƙasar, domin nuna alhinin mutuwar mutumin da ya kafa ƙasar.

An karrama gawar Nujoma kafin a yi bankwana da ita, inda aka zagaya da ita zuwa yankuna bakwai na ƙasar da suka hada da kauyensa na Etunda, da ke Okahao.

Leave a Reply