An Yi Bikin Baiwa Dalibai 350 Takardun Shaidar Kammala Horo Da Dokta Wailare Ya Dauki Nauyin Su

0
333

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

A RANAR lahadin da ta gabata ne, aka yi bikin baiwa Dalibai 350 da gidauniyar Tamallan ta dauki nauyin basu horo kan ilimin na’ura Mai Kwakwalwa takardun su na shaidar kammala karatu a wani kasaitaccen biki da ya gudana a babbar makarantar Firamare ta Dambatta.

Wakilin mu wanda ya rika duba yadda bada horon ya gudana, ya ruwaito cewa darussan da daluban suka koya ya kasance abin alfahari game al’umma duba da yadda har wasu daga cikin su suka samar da manhajoji na gudanar da bincike kan harkokin da suka shafi abubuwan da ake nemowa cikin na’ura Mai Kwakwalwa.

Wannan ta sanya al’umomin kananan hukumomin Dambatta da Makoda suke yiwa Dokta Wailare kallon matashin dan siyasa wanda yake ta kokarin kawo sauyi a yankin domin yin tafiya da zamani, sannan matasan yankin sun bayyana cewa za su ci gaba da yin dukkanin kokarin su wajen ganin Dokta Wailare ya sami nasara a zaben da za a yi na 2023 domin ya wakilci Dambatta da Makoda a majalisar wakilai ta kasa ta yadda zasu ci gaba da rabauta daga kyawawan manufofin sa.

Idan dai za a iya tunawa, Dokta Saleh Musa Wailare ya bijiro da muhimman abubuwa wadanda a yau dinnan suke amfanar mutanen Dambatta da Makoda a fannin ilimi da kula da lafiya da harkar hidima gaba addini da kuma yadda ya kawo sauyi na ci gaba a siyasar yankin wanda a yau an sami fahimtar juna tsakanin yan siyasar wannan mazaba da kuma kyautata mutunta juna koda kuwa akwai bambancin siyasa ko ra’ayi.

Baiwa matasan da suka amfana takardun shaidar kammala samun horo kan ilimin fasahar sadarwa ta zamani bayan yan kwanaki da Dokta Wailaren ya fice daga Jam’iyyar APC zuwa PDP, ya nunar da cewa matashin dan siyasar mutum ne wanda yake da kaunar al’ummar Dambatta da Makoda a duk India ya sami kansa, wanda kuma al’ummar wadannan kananan hukumomi suka jaddada cewa shi ne zasu zaba a zaben 2023 domin samun wakilci nagari.

Leave a Reply