An yi asarar dukiya ta miliyoyin naira, sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar Idumota ta Birnin Legas

0
74

Wata gobara da ta tashi a ranar Laraba, a shagunan dake ɓangarorin Nnamdi Azikiwe da Dacemo na kasuwar idumota ta jihar Legas, ta lalata dukiya ta miliyoyin nairori.
Gobarar ta shafi wasu gine-gine guda 3 ne, ciki harda wasu benaye masu hawa bibiyu da wani bene mai hawa ɗaya, a ɓangaren kasuwar daya fi shahara da kasuwancin tufafi da takalma da jakunkuna.

KU KUMA KARANTA:Shaguna 180 sun ƙone a gobarar babbar kasuwar Sokoto

Tuni dai jami’an hukumar kwana-kwana da ba da agajin gaggawa ta jihar Legas da sauran hukumomin ba da agaji suka isa wurin da al’amarin ya faru inda suka ƙaddamar da aikin kashe gobarar.

A cewar Shugabar Hukumar Kwana-Kwana ta jihar Legas, Margaret Adeseye, cibiyoyin kashe gobara na unguwannin Ebute Elefun da Ilupeju da Alausa sun tura jami’ai da kayan aiki domin taimakawa wajen shawo kan gobarar wacce tuni aka ƙaddamar da yaƙi da ita.

Har yanzu dai ba’a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma an ƙaddamar da bincike akan hakan. Haka kuma, ba’a kai ga tantance asarar rai ko jikkata ba

Adeseye ta buƙaci mazauna yankin su baiwa jami’an ba da agajin gaggawa haɗin kai tare da kaucewa wurin domin kiyaye lafiyarsu.

Leave a Reply