An tsinci yara 4, jariri da ransu, bayan kwanaki 17 da haɗarin jirgin sama a Kolombiya

0
425

Hukumomin Kolombiya (Colombia) sun gano wasu yara uku da wani jariri ɗaya a raye kwanaki 17 bayan da wani jirgin sama ya yi hatsari da su a cikin dajin da ke kudancin ƙasar.

Shugaba Gustavo Petro ne ya bayyana hakan a yammacin Larabar nan.

“Bayan zazzafar bincike da Sojojin mu suka yi, mun gano yara 4 da suka ɓace a raye sakamakon hatsarin jirgin sama a Guaviare.

“Abin farin ciki ga ƙasar,” Petro ya wallafa a shafinsa na Twitter. Har yanzu sojojin Colombia sun tabbatar da gano wasu ƙananan yara huɗu, yara masu shekaru 13, mai shekaru 9, mai shekaru 4 da kuma mai watanni 11.

KU KUMA KARANTA: Dalibi ɗan Najeriya da ke Amurka ya mutu sanadiyar haɗarin da ya yi da wani jirgin haya

A ranar Laraba da safe, sun gano wani katafaren gida wanda aka gina da sanduna da rassa a cikin daji.

Gwamnatin Colombia dai ta tura sojoji sama da 100, karnuka masu sanki da kuma ‘yan asalin yankin domin gano yaran.

Yaran na cikin wani jirgin sama mai haske na Cessna C206 lokacin da ya yi haɗari a cikin ‘Amazon’ da ke kudancin yankin Caquetá a ranar 1 ga Mayu. Manyan mutane uku da ke cikin jirgin sun mutu a haɗarin.

Leave a Reply