An tsare gomman masu zanga-zangar yaƙi da cin hanci da rashawa

0
89
An tsare gommai masu zanga-zangar yaƙi da cin hanci da rashawa

An tsare gomman masu zanga-zangar yaƙi da cin hanci da rashawa

Aƙalla masu zanga-zanga guda 30 aka kame jiya lahadi a Accra baban birnin Ghana yayin zanga-zanga nuna hushi kan kasawar gwamnati wajan magance matsala cin hanci da rashawa mai nasaba da haƙar zinari ba bisa ƙa’ida ba

An soma kamen ne da sanyin safiyar jiya lahadi lokacin da masu zanga-zanga suka so kawo cikas a ƙoƙarin ‘yan sanda na tabbatar da doka da oda kamar yadda daraktan yada labaran runduna ‘yan sanda Ghana Grace Ansah Akrofi ta sanar , tana mai  bayyana taron amatsayin wanda ya sabawa doka.

Bayan lafawa rana,  wasu gomman masu zanga-zanga sun yanke shawara  sake dawowa akan tituna.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: Kotun Tarayya ta aika mutum 10 gidan yari

Guda daga cikin masu zanga-zanga Felicity Nelson cikin hushi ta faɗa cewa, baya daga hurumin ‘yan sanda na zaba mana inda ya kamata mu gudanar da zanga-zanga hakki ne da kundin tsarin mulkin kasar ya bamu.

Waɗanda suka shirya zanga-zangar sun zargi gwamnati da tauye wa jama’a ‘yancin faɗin albarkacin baki, yayin da suka ce an kame jumullar mutane 32 ciki har da wata ƙaramar yarinya ‘yar shekaru 8 da haihuwa.

Leave a Reply