An soma jana’izar shugaban Hamas, Ismail Haniyeh

0
51
An soma jana'izar shugaban Hamas, Ismail Haniyeh

An soma jana’izar shugaban Hamas, Ismail Haniyeh

An soma gudanar da jana’izar shugaban ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Iran, bayan Isra’ila ta yi masa kisan gilla a gidansa da ke Tehran.

Shugaban Addini na Iran Ali Khamenei ne yake jagorantar sallar jana’izar Haniyeh amma daga bisani za a kai gawarsa Doha domin a binne ta.

Tun da farko Khamenei ya yi barazanar “ɗaukar hukunci mai tsauri” kan kisan.

A tsakiyar babban birnin Iran, dubban mutane ne suka riƙe hotuna da kwalaye masu ɗauke da sunana Haniyeh da tutocin Falasɗinu inda suka taru a Jami’ar Tehran University da sanyin safiyar Aalhamis, a cewar wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP.

KU KUMA KARANTA: An kashe shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a Iran

Rundunar zaratan sojojin Iran ta Revolutionary Guard ta sanar da kisan gillar da Isra’ila ta yi wa Haniyeh da mai tsaron lafiyarsa a harin da ta kai ta sama a gidansa da ke Tehran da tsakar daren Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here