An sanya dokar hana fita a Hadejia ta jihar Jigawa
Daga Shafa’atu Dauda, Kano
Rahotanni na nuni da cewa an sanya dokar hana fitar ne a Jihar Jigawa tare da samar da Shingen bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Mai Suna Zainab Ibrahim.
Matakin Ya biyo bayan taron da aka gudanar a karamar hukumar Hadejia, wanda ya haɗa jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da shugaban Karamar Hukumar Malam Madori da Kirikasamma.
Wata majiya ta rawaito cewa Manufar taron shi ne samo mafita dangane da matsalolin tsaro da ke ƙara addabar Yankin.
Da yake jawabin a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a.
Ya kuma buƙaci shugabannin yankin da su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
An tsinci gawar Zainab Ibrahim, wacce aka ɗaura mata aure a baya-bayan nan, kwance cikin jini a gidanta da ke unguwar Warware.
KU KUMA KARANTA:Zulum ya bawa jami’an tsaro kyautar gidaje da motoci a jihar Borno
Lamarin ya tayar da hankalin al’ummar yankin, Inda lamarin ya tilastawa hukumomi ɗaukar matakan tsaro cikin gaggawa.
Bayan tattaunawa, an amince da sanya dokar hana fita daga ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na Asuba, tare da kafa wuraren binciken tsaro.
Shugaban kwamitin tsaro na Ƙaramar Hukumar Hadejia, Ahmed Ari, ya bayyana cewa dokar hana fitar za ta taimaka wajen rage aikata laifuka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma roƙi al’ummar yankin su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da nasarar waɗannan matakai.