An saki tsohon Ministan Shari’an Equitorial Guinea, Ruben Maye, daga kurkuku

0
91
An saki tsohon Ministan Shari'an Equitorial Guinea, Ruben Maye, daga kurkuku

An saki tsohon Ministan Shari’an Equitorial Guinea, Ruben Maye, daga kurkuku

An saki tsohon Ministan Shari’an Equitorial Guinea Ruben Maye Nsue Mangue, wanda aka ɗaure a kurkuku tun watan Agustan bara saboda ƙiran shugaban ƙasa Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ‘shaiɗan’.

An sallame shi daga gidan yari ne bayan shugaban ƙasar ya yi masa afuwa.

Mangue, wanda malamin coci ne, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Litinin cewa an duba lafiyarsa sosai, kuma yana nan ƙalau, sannan ba a zalunce shi a kurkuku ba.

KU KUMA KARANTA: An ɗaure ɗan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda fyaɗe

“Na kuɓuta,” kamar yadda ya faɗa wa AFP ta wayar tarho, bayan afuwar ta ranar Juma’a.

An kama shi ne bayan an yaɗa wani kalami nasa a manhajar Whatsapp yana kiran shugaban ƙasar ta Tsakiyar Afirka Teodoro Obiang Nguema Mbasogo da suna ‘shaidan’ inda ya yi ƙira a yi tattaunawar haɗin kan ƙasa.

“Babu wani lauya da ya iya ziyarta ta, ba a gurfanar da ni a gaban kotu ba, an daure ni da hana ni ganin kowa,” in ji Mangue.

A watan Nuwamban 2022, Obiang mai shekaru 80, ya lashe zabe a karo na shida inda ya samu kashi 95.9 na ƙuri’un da aka jefa, wanda ya sanya Amurka shakkun ingancin sakamakon.

Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan’adam na yawan zarginsa da keta hakkokin mutane ciki har da ɗaure su. A baya ya musanta zarge-zargen.