An saki ɗaliban makarantan Kuriga da aka sace a jihar Kaduna

0
121

Rahotannin dake fitowa daga fadar gwamnatin jihar Kaduna sun yi nuni da cewa an sako gomman ɗalibai da aka sace daga garin Kuriga na jihar Kaduna.
Bayanin sako yaran makarantar na zuwa ne bayan shafe makonni biyu da ‘yan bindiga da ba’a tantance ko su wanene ba suka yi garkuwa da su a wani lamarin sace yaran makaranta da ya kasance ɗaya daga cikin sace-sacen jama’a mafi girma a Najeriya cikin shekarun baya-bayan nan a cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun gwamna Uba Sani na jihar.

An yi garkuwa da kimanin ɗalibai 287 ne a lokacin da ‘yan bindigar haye a kan babura suka bi ta kan makarantarsu, inda suka tafi da su a wani lamari da ya tayar da hankulan jama’a da ya jawo sukar gwamnatin jihar Kaduna da ma na tarayya.

Sai dai bayan shafe makonni bayan da ‘yan bindigar suka sace su, an kuɓutar da ‘yan makarantar, waɗanda galibinsu ‘yan shekara 8 zuwa 15 ne.

A cewar sanarwar da ya fitar a safiyar ranar Lahadi, gwamna Uba Sani ya bayyana farin cikin samun nasarar ceto yaran yana mai cewa ”Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, ina sanar da cewa an sako yaranmu na makarantar Kuriga da aka sace.”

Gwamnan ya kuma miƙa godiya ta musamman ga dukkan masu ruwa da tsaki musamman ma Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, jami’an gwamnati da jami’an tsaro kan rawar da suka taka wajen kuɓutar da ɗaliban.

Duk da cewa yawaitar sace-sacen ɗalibai ya ɗan ragu a ‘yan watannin baya-bayan nan tun bayan da ‘yan bindiga suka fara kai hari a kan makarantu, sace ƙananan yaran makarantar Kuriga ya sake tunawa iyaye sace ɗalibai sama da 200 da aka yi a garin Chiɓok da ke jihar Borno a watan Afrilun shekarar 2014.

Idan Ana iya tunawa, ’yan ta’adda da ‘yan bindiga sun sha kai hare-hare musamman ga ɗaliban makaranta, tun daga sace ‘yan matan Chiɓok a shekarar 2014, zuwa ga sace yaran makaranta a birnin Dapchi na jihar Yobe.

Sace yaran makaranta don neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare inda a watan Disambar shekarar 2020, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnatin maza a Ƙanƙara na jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da ɗalibai kusan 300.

KU KUMA KARANTA:Amurka ta ƙaddamar da shirye-shirye guda uku kan al’adu da ilimi a Najeriya

Watanni biyu bayan faruwar lamarin Ƙanƙara, a ranar 17 ga watan Fabrairu, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace ɗalibai 27 da wasu mutane 15 daga makarantar kimiyya ta gwamnati da ke garin Kagara a jihar Neja.

Haka kuma, a wani harin da aka kai da sanyin safiya, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai mata 317 na makarantar sakandaren mata ta gwamnati a garin Jangeɓe na jihar Zamfara.

Sannan kuma a ƙarshen watan Mayu wasu gungun mahara ɗauke da muggan makamai a kan babura suka mamaye garin Tegina da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja, inda suka yi harbi ba ƙaƙƙautawa tare da yin garkuwa da ɗalibai kusan 150 daga makarantar Islamiyyar Salihu Tanko.

A wannan karon dai Shugaba Tinubu da hukumomin sojin Najeriya, sun kasance sun ba da tabbacin cewa za a ceto yaran makarantar Kuriga da abin ya shafa, daga bisani aka sami nasarar kuɓutar da su.

Masana tsaro dai na ƙara jadada cewa dole ne a fito da sabbin dabarun kula da dazukan ƙasar domin samun sauƙi ga matsalar sace-sace gomman yara daga makarantun su.

Leave a Reply