An sake zaɓen Bola Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS

0
65
An sake zaɓen Bola Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS

An sake zaɓen Bola Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS

Daga Idris Umar, Zariya

An tsawaita wa’adin Shugaban ƙungiyar ne a taron shugabannin ƙungiyar ECOWAS karo na 65 da aka yi a ranar Lahadi a Abuja, biyo bayan matakin da Shugabannin suka ɗauka na tabbatar da dorewar zaman lafiya da samar da ci gaba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasar Najeriya kuma Shugaban ECOWAS shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Cif Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai.

Da farko dai an zaɓi Shugaba Tinubu a matsayin Shugaban Ƙungiyar a Guinea Bissau a ranar 9 ga Yulin 2023.

A jawabinsa na karɓar Shugabancin ya ce, zai mayar da hankali wajen ƙarfafa kimar dimokaradiyya da kuma tabbatar da muradun ƙungiyar da za ta cika shekaru 50 a shekarar 2025.

Shugaban ƙungiyar ECOWAS ya ayyana Shugaban ƙasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, da shugaban kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbé a matsayin jakadu na musamman da za su maido ƙasashen Burkina Faso, da Mali, da Jamhuriyar Nijar cikin ƙungiyar bayan ficewarsu.

“Zan ci gaba da ɗaukar matakan cigaba, gami da gina tsarin dimokuradiyya da tsarin da muka gada Na gode sosai ”Shugaban ya ce.

A baya dai Shugaba Tinubu ya yi kira ga shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS da su ba da himma wajen ganin an kafa rundunar da za ta samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin yankin.

KU KUMA KARANTA: Shugabannin soja na yankin Sahel suna gudanar da taro a Nijer, yayin da ECOWAS ke taro a Najeriya

Shugaban ya jaddada amfanin rundunar da za ta yi aiki tare da fuskantar barazanar tsaro a yankin.

Leave a Reply