An sake ‘yan jaridu 2 da gwamnatin Kano ta tsare

0
163
An sake 'yan jaridu 2 da gwamnatin Kano ta tsare

An sake ‘yan jaridu 2 da gwamnatin Kano ta tsare

Daga Lawan Yakasai

Rayuwar ‘yan jarida biyu a Kano na fuskantar barazana, baya ga yadda aikin Jaridar ya shiga cikin tasku, sakamakon yadda waɗanda ya kamata su ƙarfafi aikin Jarida saboda tarihinsu na Gwagwarmaya, yau su ne ke ƙoƙarin tauye ƴancin aikin Jarida.

Ƙungiyar Kare haƙƙin ɗan’Adam ta ƙasa-da-ƙasa Amnesty International ta yi tur da Allah-wadai da tozartawa, cin zarafi da yiwa wasu Ƴan Jarida biyu barazana, Buhari Abba Rano editan Jaridar Internet ta Kano Times da Isma’il Auwal, ta hanyar kamasu da Ƴan Sanda suka yi bisa umarnin Kwamishinan Yaɗa labarai na Gwamnatin Kano Ibrahim Waiya, kamar yadda Amnesty International ke zargi.

Shi dai Ɗan Jarida Buhari Abba ya samu gayyata ne daga sashen binciken manyan laifuka na rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano wato CIID, wanda daga amsa wannan gayyata ne sai aka garƙameshi na tsawon awanni.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano ta ba da umarnin cafke ‘yan jarida 2 kan wallafa wani rubutu

Wannan kamu kuma binciken da Amnesty International ta yi, ta gano cewa an yi shi ne bisa tuhumar Ɗan Jaridar da wallafa wani rubutu a Shafin Kano Times, wanda yake ƙalubalantar cin zarafi ko ɓata suna, tare da yin watsi da yunƙurin tauye ƴancin bayyana ra’ayi da kuma neman daƙile amon masu koke.

Amnesty International ta ce dole ne Gwamnatin Kano da rundunar Ƴan Sanda su girmama ƴancin kowane ɗan ƙasa na bayyana ra’ayi. Dole ne a kawo ƙarshen yunƙurin amfani da ƴan sanda wajen hukunta Buhari Abba Rano da Isma’il Auwal, tare da tabbatar da kare haƙƙoƙinsu na ɗan’Adam.

Bayan shiga tsakani ne dai ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’Adam ɗin ta yi rahotanni suka ce Ƴan Sanda sun sako Buhari Abba, kuma a tattaunawarmu da shi Mawallafin na Kano Times Buhari Abba ya ce shi fa ba shi ya kar zomon ba, rataya kurum aka bashi, amma saboda wani dalili aka nemi cimasa zarafi.

Yanzu haka dai ƙungiyoyin fararen hula da dama dake fafutuka domin kare haƙƙin ɗan Adam sun shiga wannan magana, suna ta kiraye-kiraye kan cewa lallai a yiwa tufkar hanci, kafin aikin Jarida ya gamu da babbar matsalar da za ta kaishi kushewa.

Leave a Reply