Ƙasar Saliyo ta saka dokar hana fita bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari barikin soji da kuma yunkurin afkawa sashen ajiye makamai na barikin a Freetown babban birnin ƙasar.
A wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta fitar, ta bayyana cewa tuni jami’an tsaro suka shawo kan lamarin.
Tun da farko kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa ana ta jin ƙarar harbe-harbe ba kakkautawa a cikin birnin na Freetown.
“Da safiyar Lahadi, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi yunƙurin afakawa cikin ma’ajiyar makamai da ke barikin Wilberforce. An daƙile su,” kamar yadda Ministan Watsa Labarai Chernor Bah ya bayyana a wata sanarwa.
“An saka dokar hana fita a ƙasa baki ɗaya wadda za ta fara aiki nan take. Muna bayar da shawara da babbar murya kan ‘yan kasa su zauna a cikin gida,” in ji sanarwar.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan Iran za su dawo kama matan da suka karya dokar rufe gashin kansu
Shugaba Julius Maada Bio ya jinjina wa jami’an tsaro kan daƙile harin da suka yi inda ya ce sun nuna jajircewa.
“Za mu ci gaba da jajircewa wajen ganin mun kare dimokaraɗiyya a Saliyo, kuma ina ƙira ga ɗaukacin al’ummar Saliyo da su haɗa kai domin sauke nauyin da ke kanmu baki ɗaya,” kamar yadda ya wallafa a shafin X.
“Babu abin da ya kai zaman lafiyar ƙasarmu kuma za mu ci gaba da kiyaye ƙasarmu da samar da zaman lafiya a Saliyo da kuma yaƙi da duk wasu da ke son yi wa zaman lafiyarmu zagon-ƙasa,” kamar yadda shugaban ya ƙara da cewa.