An kuɓutar da almajirai 18 da ‘yan bindiga suka sace a Sakkwato

0
166

Ɗan Majalisar dokoki ta jihar Sakkwato mai wakiltar mazaɓar Gada ta gabas Honorabul Haruna Dauda ya ce an ceto yaran ne bisa ga ƙoƙarin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da haɗin guiwar gwamnatin jihar Sakkwato.
Yace Kwamandan garison na sojojin Najeriya dake Sokoto ne ya hannunta yaran da wasu mata da aka ceto su goma sha takwas.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun sace ‘yan makarantar Allo a Sakkwato

A cewarsa, Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya umurci a duba lafiyar mutanen da aka ceto kuma dukkansu na cikin ƙoshin lafiya.

Gwamnatin Sakkwato daga bisani ta hannunta mutanen ga shugaban ƙaramar hukumar Gada da sauran shugabannin yankin domin a sadar da su da iyalansu.

Ranar Jumu’a, 8 ga watan Maris ne ‘yan bindigar suka kai samame suka sace almajiran da wasu mata a ƙauyen Gidan Bakuso a ƙaramar hukumar Gada dake gabasin Jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Leave a Reply