An kashe wata ɗalibar jami’a mai shekaru 21 bayan an yaudareta da wasu kuɗi
Daga Ali Sanni Larabawa
Wata budurwar mai shekara 21 da aka bayyana ɓacewarta tun ranar 9 ga watan Agustan 2024, an same ta babu rai a wani wajen zubda shara dake unguwar Aleniboro a Ilorin, babban birnin jihar.
Rundunar ‘yan sandar jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.
Kakakin rundunar, DSP Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa marigayiyar ta samu ƙiran waya daga wata Mis Timileyin a ranar 9 ga watan Agusta, 2024, game da wani taron da ɗaliban makarantar a Offa, da suka shirya.
Matar ta gabatar da marigayiyar ga wani Mista Adebayo Happiness, ɗaliban Jami’ar Summit, wanda ake zargin ya gayyace ta zuwa liyafar dare a kan zargin cewa tayi a matsayin budurwarsa kan kuɗi naira 15,000.
KU KUMA KARANTA: An watsa wa budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska a Zariya
“Duk da haka, marigayiya Mojisola ta sanarwa da abokiyar zamanta, wata Blessing O, cewa ta ji ba dadi a otal ɗin da Adebayo Happiness ya sauƙe ta kuma ta lura cewa babu wani biki a wajen da aka ce.
“Ba daɗewa bayan wannan tattaunawar wayarta a kashe ta kuma duk ƙoƙarin da Miss Blessing ta yi na samunta baiyi nasara ba”, in ji shi.
Tace an kama wanda zake zargin aikata kisan kuma an miƙa shi ga cibiyar binciken laifuka ta jihar.