An kashe sojoji 5 da ‘yan Boko Haram da dama a wani hari a ƙauyan Borno

0
29
An kashe sojoji 5 da 'yan Boko Haram da dama a wani hari a ƙauyan Borno

An kashe sojoji 5 da ‘yan Boko Haram da dama a wani hari a ƙauyan Borno

Aƙalla sojojin biyar ne suka mutu sakamakon wani harin ba-zata da ‘yan ta’addar ƙungiyar Boko Haram suka kai a wani sansanin soji da ke ƙaramar hukumar Gubio a jihar Borno.

Hedkwatar Tsaron Najeriya, DHQ a wata sanarwa a ranar Talata ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce sojojin waɗanda aka jibge ne don ba da kariya a yankin, kuma an kashe ‘yan ta’addar ma da dama a arangamar.

“Harin wanda shiryayye ne ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar da jikkata wasu 10, sai kuma huɗu da ba a gani ba har yanzu, sannan dakarun ma sun kawar da ‘yan ta’addar da dama tare da ƙwato makamai,” in ji daraktan watsa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba.

Mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Turkiyya na Anadolu cewa lamarin ya faru ne a ƙarshen mako a wani ƙauye, inda maharan suka jefa wa sansanin sojin bama-bamai daga ɓangarori daban-daban.

‘Yan garin sun ce sun ji ƙarar harbe-harbe daga sansanin lokacin da sojojin suke musayar wuta da ‘yan Boko Haram din, inda bayan awanni ‘yan ta’addar suka sake kai harin har ma suka jikkata wasu fararen hula.

KU KUMA KARANTA: Harin Boko Haram ya kashe sojojin ƙasar Chadi sama da 40

Sanarwar DHQ ta ƙara da cewa ‘yan Boko Haram din sun kuma ƙona motar igwa ta sojoji da sauran wasu kayan yaƙin.

“Kazalika an tura wata tawagar sojin sama don karaɗe illahirin yankin da kuma gano hanyar da ‘yan ta’addar ke bi,” in ji Manjo Janar Buba.

Rundunar sojin ta ce yana da muhimmanci a fahimci cewa wannan harin ba zai kawar da hankalin dakaru da kuma rundunar sojin Najeriya daga ƙoƙarin kawo ƙarshen ta’addanci da tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar ba.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga rundunar sojin ƙasar yana mai cewa wannan hari tunatarwa ce ga jihar kan irin rashin kan-gadon ‘yan ta’addar Boko Haram.

Leave a Reply