An kashe shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a Iran

0
119
An kashe shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a Iran

An kashe shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a Iran

An kashe shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar da kuma jami’an gwamnatin Iran suka fitar.

Hamas ta ce Isra’ila ce ta kashe shugabanta ranar Laraba da sanyin safiya a samamen da ta kai a gidansa da ke Tehran.

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta bayyana juyayin rasuwar Haniyeh, mai shekara 62, wanda “miyagu masu tsananin kishin kafa ƙasar Isra’ila” suka kashe a gidansa da ke Tehran.

Haniyeh, wanda fitacce ne a fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawam ya daɗe yana gwagwarmaya kan kisan ƙare-dangin da Isra’ila take yi a Gaza.

Gwamnatin Iran ta ce ta ƙaddamar da bincike kan kisansa, wanda take sa ran fitar da sakamakonsa nan ba da jimawa ba.

KU KUMA KARANTA: Hamas ta amince da shawarar Qatar da Masar ta tsagaita wuta a Gaza na — Haniya

“An kai hari a gidan shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, Ismail Haniyeh a Tehran, kuma sakamakon hakan shi da ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa sun yi shahada,” in ji wata sanarwa da shafin intanet na Sepah, mallakin rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps ya wallafa.

Kawo yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin kisan, sai dai ana zargin Isra’ila da aikata shi, domin kuwa ta daɗe da shan alwashin kashe Haniyeh da sauran shugabannin ƙungiyar Hamas.

Leave a Reply