Daga Ibraheem El-Tafseer
Wani matashi mai sana’ar tuƙa Keke-Napep a garin Potiskum jihar Yobe, ya gamu da ajalinsa sakamakon caccaka masa wuƙa a ciki da sara da adda akai da wasu da ake zargin ɓarayin Keke Napep ne suka yi masa a ranar Talata da ta gabata.
Shi dai wannan matashi mai suna Nazir Ɗanliti, mai shekaru 23, wanda ke zaune a unguwar Tandari, a cikin garin Potiskum, yana sana’ar tuƙa Keke-Napep wasu da ake kyautata zaton ɓarayi ne suka kashe shi, suka gudu da Keke-Napep ɗin.
Mohammed Mukhtar Umar, ƙanin mahaifiyar Nazir, ya shaida wa Neptune Prime Hausa cewa “Nazir ya fita sana’arsa ta tuƙa Keke-Napep a ranar Talata, sai aka ga lokacin dawowarsa ya yi, amma shiru bai dawo ba. Abu dai kamar wasa, har gari ya waye bai dawo ba. To sai aka fita nemansa, wajajen ƙarfe 9:00 na safe sai aka tsinci gawarsa an kashe shi, an gudu da Keke Napep ɗin, a bye-pass na hanyar Damaturu (Hawan Malka) Sun caccaka masa wuƙa a ciki ne, sannan sun sassara kansa da adda”.
KU KUMA KARANTA: Ɗan fashin mota ya kashe jami’in kwastam a Kebbi
Jami’an tsaron ‘yan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin, suna nan suna ci gaba da bincike don zaƙulo waɗanda suka yi masa wannan kisan gilla. Mahaifin Nazir ya rasu, amma mahaifiyarsa tana raye, ta ce ta bar komai a hanun jami’an tsaro har Allah ya sa a yi nasarar kama waɗanda suka kashe shi. Inji ta.
[…] KU KUMA KARANTA: An kashe matashi, an gudu da Keke-Napep ɗinsa a Yobe […]