Connect with us

Ƙasashen Waje

An kashe fiye da mutum 60 a rikicin ƙabilancin ƙasar Papua, New Guinea

Published

on

Ƴan sanda sun sun ce an gano gawawwaki 64 da aka yi musu jina-jina zube a kan wata hanya a wani yanki yanki mai nisa a Papua New Guinea, abin da ke nuna cewa ƴaƙin da aka jima ana yi tsakanin ƙabilun yankin na ƙara ƙazancewa.

An yi amanna cewa, mutanen da aka kashe mayaƙan wata ƙabila ne, da mayaƙan wata ƙabilar daban suka yi wa kwanton ɓauna ranar Lahadi.

Lamarin ya faru ne a kusa da garin Wabag, kimanin kilomita 600 arewa maso yammacin babban birinn ƙsar Port Moresby.

Kwamishinan ƴan sanda David Manning Monday ya bayyana lamarin a matsayin wani “gagarumin dabbanci”, sannan ya bayyana cewa ana shirin gudanar da wani “aiki na musamman” a yankin, don “mai da doka da oda.”

“An bai wa waɗannan jami’an umarni a fayyace cewa su yi amfani da kowane irin ƙarfi da ake buƙata don hana sake faruwar irin wannan tashin hankalin, yana mai cewa, “Wannan ya haɗa da amfani da ƙarfi fiye da ƙima idan aka yi wa rayuwar jami’an tsaro da ta fararen hula barazana.”

KU KUMA KARANTA: Afirka ta Kudu za ta tura dakaru 2,900 don yaƙi da ƴan bindiga a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

Yankin wanda ke fama da tashin hankali tsawon shekaru, ya zama wani wajen ramuwar gayyar kashe-kashe tsakanin ƙabilun Sikin, da Ambulin da wasu ƙabilun.

Wasu hotuna masu tada hankali da ƴan sanda suka fitar daga wajen da lamarin ya faru, sun nuna gawawwaki jina-jina kwance a gefen titi, sannan an loda wasu a bayan wata motar ɗaukan kaya.

Wasu mutanen an cire musu wasu gaɓoɓi, sannan wasu ba kaya a jikinsu, yayin da aka ɗaura musu kwalabe ko gwangwanaye a ƙirjinsu.

A ranar Litinin, ƴan sanda sun ce an ringa jin ƙarin bindiga a wani waje kusa da inda lamarin ya faru, kuma an ci gaba da gano wasu gawawwakin daga dazukan da ke kusa da hanyar.

“Mun yi amanna cewa akwai wasu gawawwakin a cikin daji, a cewar mataumakin kwamishinan ƴan sanda Samson Kua.

An shafe ɗaruruwan shekaru ƙabilu na faɗa da juna a yankin na Papua New Guinea, amma ƙaruwar sojojin haya da bazuwar makamai masu sarrafa kansu, sun sa faɗace-faɗacen sun ƙara ƙazancewa, sannan an ƙara samun yaɗuwar tashin hankalin cikin gaggawa.

Kua ya ce ƴan bindigar na amfani da muggan makamai, da suka hadar da bindigogi samfurin SLR, da AK-47, da M4, da AR15 da kuma M16, sai kuma bindigar harba-ruga da bindigogin da ake ƙerawa a gida.

Muƙaddashin kwamandan ƴan sandan yankin, Patrick Peka yace da dama daga waɗanda aka kashe ɗin sojojin haya ne – waɗanda suke yawo a yankin suna tayin taimakawa ƙabilu taimaka musu wajen ɗaukan fansa a kan abokan gabarsu.

“Ƴan sanda da gwamnati ba za su iya yin wani abin a-zo a-gani ba lokacin da shugabanni da masu faɗa-a-ji suke safarar makamai, sannan suke daukan sojojin haya daga wasu sassan yankin,” a cewar Peke.

Gwamnatin Papua New Guinea ta yi kokarin daƙile rikicin, da shiga tsakani, da yin afuwa da ma wasu matakan don taƙaita yaɗuwar rikicin, sai dai babu wata nasarar a zo a gani.

Rundanar soja ta tura fiye da sojiji 100 yankin, sai dai tasirinsu taƙaitacce ne, sannan mayaƙan ƙabilu sun fi jami’an tsaro yawa sun fi su makamai.

A mai yawan lokuta, an fi samu kashe-kashe ne a yankuna masu nisa, inda ake kai farmaki da kwanton ɓauna a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da aka kai a baya.

A baya an sha kai farmaki kan fararen hula da suka haɗa da mata masu ciki da ƙananan yara.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Published

on

Harin ta'addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Wani hari da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne suka kai ƙauyen Djiguibombo da ke kusa da garin Bandiagara a yankin tsakiyar ƙasar Mali, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 20, kamar yadda wasu hukumomin yankin biyu suka tabbatar.

Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu sun tabbatar da mutuwar mutane 20, sannan suka ce yadda lamuran tsaro suka taɓarɓare a yankin, ya hana jami’an tsaro kai ɗauki wajen.

Wani jagoran matasan yankin shi ma da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun a farkon daren ranar Litinin ɗin data gabata ne maharan suka kai farmakin, inda suka kwashe tsawon sa’oi uku a cikin garin.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami’ai

Ya ce sama da mutane 20 ne aka kashe a harin, kuma fiye da rabinsu matasa ne inda aka ranke musu harsuna.

Kasar Mali dai na fama da matsalolin tsaro na ƙungiyar Al-Qaeda da kuma na IS tun a shekarar 2012, inda ya bazu kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da ita.

Tun bayan ƙwace mulki da sojoji suka yi a kasar a shekarar 2020, hukumomi  ke jin tsoron fitowa fili su sanar da labarin hare-haren ta’addancin da ake kai wa kasar da ke Yammacin Afrika.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Published

on

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama - Ministan Tsaron Isra'ila

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce sojojin Isra’ila za su kasance a shirye don daukar duk wani matakin da ya dace kan ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon, ko da yake abin da ake so shi ne cimma matsaya ta shawarwari.

Muna kai wa ƙungiyar Hizbullah hari sosai a kowace rana kuma za mu kai ga cikakken shiri na ɗaukar duk wani mataki da ake buƙata a ƙasar Labanon, ko kuma cimma wani shiri daga matsayi mai ƙarfi.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

Mun fi son tsari, amma idan aka kai mu maƙura za mu san yadda za mu yi yaƙi,” an ruwaito Gallant a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Published

on

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Aƙalla mutum 12 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a jiya Laraba a wani hari da aka kai kan wata kasuwar dabbobi da ke El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Yammacin Sudan.

A wata sanarwa da kwamitin sulhu na kwamitocin ‘yan gwagwarmaya na El Fasher ya fitar ya ce “harbin bindigogi a kasuwar dabbobi da ke birnin El Fasher ya yi sanadin mutuwar fararen hula 12 da kuma wasu 20 da suka samu raunuka daban-daban.”

Tun da fari a ranar Larabar da safe, kwamitocin ‘yan gwagwarmaya sun ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai mummunan hari El Fasher da manyan bindigogi.

Tun a ranar 10 ga Mayu, aka fara ƙazamin fada tsakanin sojojin Sudan da RSF a El Fasher. Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ke amfani da birnin a matsayin cibiyar ayyukan jinƙai ga yankin Darfur.

Rikicin Sudan ya ɓarke ne a cikin watan Afrilun 2023 tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan yarjejeniyar shigar da RSF cikin rundunar soja.

KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

Ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 16,000, da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, sannan sama da miliyan 25 na buƙatar agajin jinƙai, lamarin da ya zama mafi girma a duniya ta ɓangaren matsalar rashin matsuguni da yunwa, a cewar MƊD.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like