An cafke wata budurwa ’yar shekara 20 tare da saurayinta da buhuna biyar na tabar wiwi a jihar Edo.
’Yan sanda sun cafke budurwar da saurayinta mai shekaru 40 ne a gidan da suke zama a unguwar Ologbo a Ƙaramar Hukumar Ikpoba-Okha.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Edo, Chidi Nwabizor, ya ce, rundunar ta yi nasarar cafke su ne bayan makwabtaka sun kawo rahoton zargin masoyan suna tara ganyen tabar wiwi a cikin gidan.
Bayan an kai samame gidan ne kuma aka gano buhuna biyar na tabar wiwi a ciki.
Jami’in ya ce rundunar ta kuma kama wasu mutane huɗu kan zargin fasa wani turken sadarwa na kamfanin Airtel, da sace baturansa da kuɗinsu ya kai naira miliyan 12 a garin Benin, babban birnin jihar.
Ya ce an cafke su ne a cikin motarsu bayan sun je shan mai a wani gidan mai, amma da aka bincika motar ba a ga alamar kayan laifi a cikinta ba.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure wani tsoho mai shekaru 82 da wani matashi kan laifin tabar wiwi
Ya ce waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifin, duk da cewa rundunar ta samu ƙiran neman agaji da ke nuna cewa su ne suka sace batiran.
Don haka ya ce za a ci ca gaba da bincike kan lamarin.