An kama wasu ‘yan Shi’a a Abuja kan zargin kisan jami’an tsaro

0
51
An kama wasu 'yan Shi'a a Abuja kan zargin kisan jami'an tsaro

An kama wasu ‘yan Shi’a a Abuja kan zargin kisan jami’an tsaro

Har yanzu ta na kasa ta na dabo game da rikicin ‘yan Shi’a da ‘yan sandan a Abuja, Najeriya. Hasali ma, ‘yan an damke ‘yan Shi’a kusan 100 don binciken zakulo masu hannu a kisan ‘yan sandan.

Biyo bayan umarnin da Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya ya bayar na kamo ‘yan Shi’a da ake zargi da kashe jami’an ‘yan sanda guda biyu, kawo yanzu kimanin wadanda ake Zargi casa’in da bakwai ne suka shiga hannu.

A dai ƙarshen makon jiya ne aka sami wani ɗauki ba daɗi tsakanin ‘yan sanda da ‘yan Shi’a masu tattaki a tsakiyar Birnin Abuja.

‘Yan sandan sun ce ‘yan Shi’a ne su ka abka wa jami’ansu ba tare da wani dalili ba, inda suka hallaka guda biyu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Katsina sun kama matashin da ya sare hannun ƙanin mahaifinsa

Ƙarin wasu da dama kuma suka sami munanan raunuka. Mai magana da yawun Rundunar ‘yan Sanda, Shiyyar Abuja, SP Josephine Ade, ta shaida wa Muryar Amurka cewa ‘yan Shi’a ɗin sun yi amfani da duwatsu, adduna, bam ɗin kwalba da sauran miyagun makamai wajen farma jami’an na su a unguwar Wuse.

Tun ma a ranar an kama kimanin ‘yan shi’a saba’in da biyar kuma har yanzu ana ci gaba da kakkamo su don su fuskanci hukunci.

To amma a ɓangarensu, ‘yan shi’ar sun ce ‘yan sandan ne su ka fara takalarsu yayin da suke kan yin tattakin da su ka saba.

Su ka ce dama ‘yan sandan sun saba yin ma su haka tun a lokutan baya can.
Sun yi zargin cewa ‘yan sandan sun abka masu inda suka hallaka masu ‘yan uwa ba laifin tsaye ba na zaune, wanda hakan ne ya harzuka su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here