Wani sojan bogi da yayi yunƙurin shiga jirgin sama na soji, ya shiga hannu bayan da sojoji suka kama shi a sansanin soji na Burma a lokacin da yayi shiga irin na Laftanar Kanar, kuma yake kokarin karɓar tikitin jirgi a sansanin sojin saman domin zuwa Tamale.
A wata sanarwar manema labarai a ranar Laraba, 7 ga watan Disamba, 2022 ta hannun hukumar kula da hulda da jama’a ta rundunar sojojin Ghana ta ce wanda ake zargin ya bayyana sunan sa da Rufa’i Abubakar.
“Wanda ake zargin da ya shiga sansanin Burma a cikin motar haya, an sanya masa ido sosai a lokacin da ya sauka a tashar motar bas ya nufi sansanin sojin sama. Masu gadin da ke bakin aiki,ba su yadda da yanayin shi ba, suka yi masa tambayoyi kuma ya kasa bada amsa gamshashiya,daga baya ya ce shi ba ma’aikacin soji bane.
KU KUMA KARANTA:Yan sanda sun kama uwa da ‘yarta bisa zargin kisan saurayinsu
“Ya kuma bayyana cewa yayi shiga a matsayin Babban Hafsan Soja ne, domin ya samu damar damfarar wani mai suna Abdallah Abdul Fatahu wanda ya karbi kudin Ghana Cedis Dubu Uku (GH03,000.00) a wajensa bisa alƙawarin ɗaukar shi aikin sojan Ghana.
“Wanda ake zargin yana sanye ne da kakin soja, wanda aka yi masa ado da mukamin Laftanar Kanar na bogi, ya yi ikirarin cewa an ajiye shi ne a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Arewa kuma yana kan hanyarsa ta zuwa sansanin sojin sama domin yin tikitin jirgi zuwa Tamale,” in ji sanarwar.
An kuma sami takardun shaidar soja na bogi da katunan kasuwanci da wasu takardu masu ɗauke da sunansa a lokacin da aka kama shi.
Daga nan ya kai jami’an ‘yan sandan Sojoji wasu gidaje guda biyu inda suka gano wasu takardu da suka hada da takardun shaida, da dama da kuma rahotannin daukar aikin GAF na bogi da ke ɗauke da sunayen waɗanda aka damfara, kayan sojoji da kayan kwalliya da bindigar wasan yara.
An mika shi ga hukumar binciken manyan laifuka (CID) na hukumar ‘yan sandan Ghana domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi gaban kuliya.
Sanarwa, ta yi kira ga jama’a da su kai rahoto ga hukumar ta CID idan wani ya taɓa faɗawa cikin tarkon wanda ake zargin.
“Duk da haka, idan aka yi la’akari da cewa matan wanda ake zargi guda biyu da ke zaune a Ablekuma da Olebu suna tunanin mijin nasu jami’in soja ne na gaske, mai yiyuwa ne wasu mutane da dama sun faɗa cikin da yaudarar sa.”
Kasancewar matan wanda ake zargin suna tare da shi, Allah kadai ya san tsawon lokacin da ya ɗauka ba tare da sanin cewa shi ba hafsan soja ne na gaske ba abin mamaki ne. Amma kuma ya nuna irin kokarin da ya yi a cikin ayyukan damfara a kullum don rufa wa kansa asiri.