An kama wani matashi a Adamawa kan lalata taransifoma

0
39
An kama wani matashi a Adamawa kan lalata taransifoma

An kama wani matashi a Adamawa kan lalata taransifoma

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Adamawa, ta kama wani matashi mai shekara 24, Auwal Sale, kan zarginsa da hannu wajen lalata na’urar taransfoma da kuma satar mai.

Kwamandan hukumar a jihar, Ibrahim Mainasara, ya ce an gano wanda ake zargin yana da galan 10, wanda huɗu daga ciki ke ɗauke da man taransifoma.

Ya ce ana zargin ya haɗa kai da wasu mutane, ciki har da wani mai suna Daddy, wanda ta tsere wajen aikata laifin.

KU KUMA KARANTA: An dakatar da Hakimi da kansila bisa zargin satar Taransifoma a Gwambe

A cewarsa, yayin bincike rundunar ta gano wani mutum da ake kira Alhaji, daga ƙaramar hukumar Song na da hannu wajen sayen man da suke satowa.

Ya ce da zarar sun kammala bincike za su miƙa wanda ake zargin zuwa kotu.