An kama masu ƙwacen waya 26 a Jigawa

0
236

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutum 26 da ake zargi da aikata ƙwacen wayoyi da kuma shan muggan ƙwayoyi.

Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Dutse.

Ya ce kamen ya biyo bayan wasu jerin samame da suka kai a tsakanin ranar 18 zuwa 19 ga watan Disamba, a ƙananan hukumomi hudu na jihar.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama ƙwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben Kodin kusan 100,000

Kakakin ya ce jami’an rundunar sun kama wani matashi kan zargin satar waya da kuma sata kuɗi baira 10,000 a garin Babura da ke ƙaramar Hukumar Babura.

Kazalika, sun kama wasu mutum biyu kan zargin laifin satar kwamfutoci shida da babur a Hadejia.

Leave a Reply