An kama manyan jami’an gwamnati kan baɗakalar kuɗin magungunan ƙananan hukumomi

0
85
An kama manyan jami’an gwamnati kan baɗakalar kuɗin magungunan ƙananan hukumomi

An kama manyan jami’an gwamnati kan baɗakalar kuɗin magungunan ƙananan hukumomi

Daga Shafaatu Dauda, Kano

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama manyan jami’an gwamnatin jihar, kan zargin baɗakalar kuɗin maganin ƙananan hukumomi.

Cikin jami’an da hukumar ta kama sun haɗa da, babban sakataran ma’aikatar ƙananan hukumomi, Ibrahim Muhammad Kabara, da kuma shugaban ƙaramar hukumar Tarauni, wanda shine shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ƙasa reshen jihar Kano (ALGON), Abdullahi Ibrahim Bashir, da kuma wasu mutane biyar, da ake zarginsu da hannu a baɗakalar kwangilar magungunan ƙananan hukumomi 44.

Haka zalika hukumar ta aike da takardar gaiyata ga shugaban rukunin shagunan magani na NOVEMED, wanda ɗa ne wurin tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.

KU KUMA KARANTA: Jami’an lafiya sun gurfana a gaban kotu a Kano bisa laifin yi wa yarinya ‘yar shekara 9 fyaɗe

Hukumar na tuhumar waɗannan mutane da saɓawa dokokin tsarin aikin gwamnati, ta hanyar aiwatar da kwangilar da bata cika ƙa’ida ba, ba tare kuma da sahalewar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ba.

Wata majiya na cewa, tuni shugaban ALGON kuma shugaban ƙaramar hukumar Tarauni, ya amsa laifin sa, inda ya tabbatar da cewa, ya bayarda da umarni ba bisa ƙa’ida ba, na biyan sama da naira milliyan 402 cikin kuɗaɗen siyan magunguna ga ƙananan hukumomin jihar.

Leave a Reply