Daga Ibraheem El-Tafseer
Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta janye jami’anta na kwantar da tarzoma waɗanda ke aikin kare wasu tsofaffin jami’an gwamnatin ƙasar ciki har da mai ɗakin tsohon shugaban Najeriya Aisha Buhari da Mallam Mamman Daura da tsohon ministan ‘yan sanda, Maigari Dingyaɗi.
Sauran mutanen da abin ya shafa sun haɗa da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Iyorchia Ayu, tsohon shugaban majalisar dattawa.
KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yan sandan a Osun za ta hukunta jami’an da ke gudanar da ayyukan cikin gida ga jami’an gwamnati
Gidan talabijin na Channels wanda ya ruwaito wata sanarwa daga Hedikwatar rundunar ‘yan sandan ƙasar tana cewa umarnin ya fara aiki nan take.
A cewar hukumomin, wannan matakin na zuwa ne a ci gaba da tantancewa da sake tsara bayanan tsaro da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke yi.
Hakan kuma na da nufin inganta jami’an ‘yan sanda da ake aike wa da kuma tabbatar da yin amfani da kayan aiki yadda ya kamata don shawo kan ƙalubalen tsaro da ake fama da shi a ƙasar.
[…] KU KUMA KARANTA: An janye ‘yan sanda masu gadin tsofaffin jami’an gwamnatin Buhari […]