Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar kula da zirga-zirga ababen hawa ta jihar (KAROTA) ta haramta wa matuƙa baburin Adaidaita hahu bin manyan titunan jihar daga ranar Laraba 30 ga watan Nuwamba, 2022.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin da za su dinga ɗaukar al’umma a titinan da aka haramtawa yan adaidaita sahun bi.
A sanarwar da jami’in yaɗa labarai na hukumar KAROTA ya fitar, ya bayyana cewa an haramta wa direbobin baburin adaidaita sahun bin titinan Amadu Bello/Mundubawa zuwa Gezawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.
Sanarwar ta ce gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin sauƙaƙawa al’umma bin waɗannan hanyoyi.
Gwamnatin ta ƙara da cewa za ta sanar da ranar da matuƙa adaidaita sahun za su daina bin wasu ƙarin manyan titinan da zarar gwamnatin ta samar da ababen hawan da al’umma za su yi amfani da su a waɗannan hanyoyi.