An Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Da Fadakarwa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Gundumar Rigasa

0
354

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A SAKAMAKON ire-iren kalubalen rashin tsaro daya ta’azzara kuma yake neman ya addabi yankin Gundumar Rigasa Kaduna, wasu al’ummar yankin sun gudanar da taron karawa juna sani da Fadakarwa bisa irin halin da al’ummar yankin da Gundumar ke fuskanta na rashin tsaro domin dakike duk wani yunkuri na ta’addanci da yan Ta’adda.

Taron wanda ya gudana a ranar Asabar a dakin taro na Sahaba dake Karshen Kwalta a garin Rigasa Kaduna, an shirya ne da zummar karawa juna sani, wayar da kai, Jan hankali da fadakar da al’ummar yankin wadanda da suka hada da Jami’an tsaro, Sarakuna, Yan Kasuwa, da masu ruwa da tsaki dake Gundumar.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar PCRC na Ofishin yan Sandan Rigasa, Alhaji Ali Makama, ya bayyana rashin Jindadinsu bisa ga irin yadda al’amura suka kara tabarbarewa a yankin dukda irin kokarin da suke tare da hadin gwiwar Jami’an tsaro yan Sanda, yan Sa-Kai da sauran al’ummar garin.

Acewarsa, a yanzu wannan wani al’amari ne da yake bukatar mutanen gari su kara jajircewa, sa-ido da yin addu’o’i wajen ganin cewa al’amura sun daidaita domin a halin da ake ciki, Jama’ar yankin na cikin wani kalubale na tashin hankali wanda ya ke barazana da tarwatsa zaman lafiya da kwanciyar hankalinsu.

Ya ce “Samun tashar Jirgin kasa a yankin wani babbar dama ce da ci gaba a gare mu amma ta wani bangaren matsala ce domin duk wanda yake son ya taba Gwamnati ta hanyar hakan za su yi amfani domin saka mana ido da yin wata barnar da za a bata mana sunan gari, don haka dole mu tashi tsaye wajen yin addu’ar neman kariyar Ubangiji.

“A cikin sati daya mun samu labarin faruwar abubuwa daban-daban wadanda suka hada da tashin Bam da wadanda aka yi nasarar cirewa, sannan kuma ga wani bala’in daya same mu na yaranmu dake aikin babban Bola na neman karfe ko yan gwangwan wanda da sassafe za kaga yaro ya dauki buhu ya kama yawo a gari, don haka dole mu ja kunnensu gudun kar garin neman karafunan su je su dauko mana abin da zai halaka mu.”

Hakazalika, da yake mayar da martani bisa ire-iren kalubalen daya addabi yankin, Hakimin Gundumar Rigasa, Alhaji Muhammad Aminu Idris Dan Galadiman Zazzau, ya buƙaci iyaye musamman maza da su dauki nauyin da Allah Ya dora musu da mahimmanci domin ta hanyar hakan ne za a iya rage wasu kalubalen da ake fuskanta.

Da yake wakiltar Hakimin Gundumar a wajen taron, Abubakar Galadima, ya kara da cewa, masu Sarautun Gargajiya na da rawar da zasu taka wanda ya hada da nuna kin amincewarsu da duk wanda basu yarda da shi ba, kana da kai rahoton duk abin da basu gamsu da shi ba tare da neman hadin kan Jami’an tsaron Gundumar da akoyaushe a shirye suke su bada irin tasu gudunmuwar.

Abubakar, ya ci gaba da cewa ya kamata Shugabannin Kungiyoyin yan Kasuwa da direbobin ababen hawa dake Gundumar su fitar da wani tsari ta yadda zasu rika lura da zagayen wuraren da suke gudanar da harkokin su domin ta haka ne zasu kara sa-ido a kan duk wasu abubuwan, kana su fahimci wani abun da basu gamsu da shi ba domin kai rahoton abin da basu aminta da shi ba musamman a irin wannan lokacin da ake tunanin miyagu sun shigo cikin Jama’ar yankin.

A karshe, taron wanda aka shirya da niyyar farkar da al’ummar yankin, ya samu halartar Baturen Ofishin yan Sanda na Rigasa da Nariya wadanda aka jinjinawa bisa namijin Kokarin da suke a Gundumar ta Rigasa Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here