An gano ɗaya daga cikin Masallatai da suka fi tsufa a duniya

0
279

Masana ilimin albarkatun ƙasa a Israila sun gano wani masallaci, da ake tunanin na ɗaya daga cikin masallatan da suka fi tsufa a duniya.

Ƙaramin Masallaci ne da aka gina da duwatsun da aka yi a tun ƙarni na bakwai.

An gano masallacin ne yayin da ake aikin gina wani rukunin gidaje a birnin Rahat da ke kudancin Isra’ila.

Kazalika, alƙiblar masallacin ta karkata ne zuwa birni mai tsarki na Makka.

KU KUMA KARANTA: Ƙwaro mafi kururuwa a duniya

Masallacin kuma na da nisan kilomita Biyu ne daga wani Masallacin irinsa, da ake tunanin an gina su ne lokaci guda, wadda aka gano a shekarar dubu biyu da goma sha tara (2019).

Leave a Reply