An yi jana’izar wasu ma’aurata da masu garkuwa da su suka kashesu, duk da biyan kuɗin fansa.
Mutumin, Mista Emmanuel Chukwuemeka, mai shekaru 36, da matarsa, Mrs Chinwendu Chukwuemeka, mai shekaru 30, wasu da ba a tantance ba ne suka yi garkuwa da su tare da kashe su. An binne su ne a garinsu da ke Isiekwulu, Ukpo, a ƙaramar hukumar Dunukofia ta jihar Anambra a ranar alhamis. Jana’izar nasu ya jefa al’ummar yankin cikin makoki.
An ce ma’auratan suna komawa gidansu ne, bayan sun halarci wani shiri a Holy Ghost Adoration da ke Uke, a ƙaramar hukumar Idemili ta arewa, lokacin da aka yi garkuwa da su.
KU KUMA KARANTA:Masu garkuwa da mutane sun kashe wani ɗan kasuwa bayan karɓar kuɗin fansa
Rahotanni sun nuna cewa ma’auratan na tare da jaririnsu ɗan wata huɗu, wanda masu garkuwa da mutane suka bar shida a cikin mota, yayin da suka tafi da iyayensa.
Wata majiya ta ce da farko ‘yan uwansu sun biya masu garkuwa da mutanen kuɗi naira miliyan 5, amma sai masu garkuwar suka buƙaci a ƙara musu naira miliyan biyu da rabi lamarin da ya ɗauki lokaci a kafin a tara, saboda sai da suka sayar da wani ɓangare na filayensu domin tattara kuɗin.
Masu garkuwa da mutanen, bayan sun karɓi kuɗin fansar da suka buƙata sun kashe wayoyinsu. Bayan kimanin watanni biyu, al’ummar garin sun ga gawarwakin ma’auratan a kan hanyar Uke zuwa Nnobi, inda aka ɗaure gawarwakin da sarƙoƙi.
[…] KU KUMA KARANTA:An gano gawarwarkin ma’auratan aka sace watanni biyu bayan an biya N7.5 kuɗin fansarsu […]